Firaministan Senegal ya kai ziyara Mali, daya daga cikin Kungiyar Kawancen Kasashen Sahel, kungiyar da aka kafa a watan Yulin 2023 a matsayin kishiya ga Kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da Mali take mamba.
Wannan ce ziyara ta farko da Sonko ya kai wata kasa tun bayan fara mulki, kamar yadda kafar yada labarai ta Mali ta rawaito kuma wasu makusantan gwamnatin Senegal suka tabbatar.
Bayan ganawa ta ''yan'uwantaka' da 'gaskiyar zance' tare da shugaban mulkin sojin Mali Assimi Goita, Sonko ya ce Sanagal da Mali na da hadin kai idan aka zo batun "Batutuwan da suke bukatar mu ci gaba da hadin kai a dukkan matakai", in ji tashar yada shirye-shirye ta Mali ORTM.
An rawaito Sonko na cewa "Zan bar nan da yakinin cewa muna da fahimta iri guda kan yadda ya kamata dangantakarmu ta kasance."
Ziyarar Firaministan na Senegal zuwa Mali ta biyo bayan halartar rantsar da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame.
Sonko ya samu tarba ta musamman daga Firaministan Mali Choguel Kokalia Maiga, in ji ORTM.
Ziyarar na zuwa ne bayan da a watan Mayu Shugaba Bassirou Diomaye Faye ya ziyarci Mali inda ya ce yana son dawo da kasar kawancen ECOWAS.
An rawaito Sonko na tabbatar wa da Bamako cewa "babu wani da zai yi amfani da Senegal wajen tayar wa da Mali hankali ko ya saka wa kasar takunkumi," ya kuma soki 'takunkumin da sauran kasashen yankin ciki har da kasarsa suka saka wa Mali" a lokacin Shugaba Macky Sall.
ECOWAS ma ta saka wa Mali takunkumi bayan juyin mulkin da ya ɗora Goita a kan mulki a 2020, amma ta janye shi bayan shekaru biyu.
"Dole ne manufar duk wani mai kishin Afirka ta zama hade kan 'yan Afirka ba tare da duba ga bambance-bambance da suke da shi ba," in ji Sonko.
A watan Janairu, Mali da Nijar da Burkina Faso sun sanar da ɓallewa daga ECOWAS, suna masu zargin kungiyar da 'yar amshin shatar Faransa, kuma ba ta yin yadda ya kamata wajen yaƙar masu tayar da kayar baya - babbar matsalar da ke addabar yankin Sahel.
Senegal na da iyaka ta kusan kilomita 500 da Mali kuma suna da manyan dangantakar tattalin arziki da al'adu ta bangaren arewaci.
Sakamakon hakan ne tsawon lokaci Dakar ke nuna damuwa game da halin tsaro a Mali da ma yankin na Sahel, tana tsoron yaduwar sa a Senegal.