RIkicin Sudan ya janyo yaduwar labarun karya game da kasar / Photo: AA

Daga Kevin Philips Momanyi

Yayin da rikicin Sudan ke ci gaba da haifar da asarar rayuka, wata babbar matsala da ke da alaka da rikicin shi ne na yaduwar labaran bogi a kafofin sadarwa.

Kafofin sada zumunta na zamani sun zama dandalin yaduwar labaran karya da labaran bogi, musamman a yankunan da ake fama da rikici.

Ana yawan ganin wannan matsalar a rikicin Sudan da ke gudana tsakanin sojoji da rundunar kawo daukin gaggawa ta kasar.

Ana zargin cewa yada labaran karya yana rura wutar rikicin, da iza gaba, da zuzuta fitintinu, musamman wadanda a kan yada su a shafukan sada zumunta.

TRT Afrika ta bi diddigin wasu bidiyoyi da suka watsu sosai a zaurukan sada zumunta, wadanda suke nuna "wai" yadda ake fafata yaki a Sudan.

Binciken namu ya nuna cewa bidiyoyin daga wani wuri daban aka dauko su, ba daga Sudan ba.

Wai an ga sojin Sudan suna rusa hedikwatar RSF?

Wani sakon bidiyo a Twitter da aka ce yana nuna sojin Sudan suna rusa hedikwatar rundunar ‘yan tawayen RSF, ya tabbata cewa na karya ne.

A bidiyon na asali wata tasha mai suna Ana_Al_Fahad ta dora shi kan YouTube, a Yemen shekara biyu da suka wuce.

Ana iya ganin rubutu ruwan hoda inda aka rubuta "@Ana_Al_Fahad" a kasan bidiyon daga gefen dama.

Wasu ba sa tantance labarai da hotuna da bidiyoyi kafin su yada /Hoto: Twitter

Wai zaki ya tsere? Bari mu bi diddigi!

Wani bidiyo a sakon Twitter ya yi ikirarin cewa wani zaki ya tsere daga gidan ajiye namun daji, kuma wai an gan shi yana sintiri a titunan Khartoum babban birnin Sudan, yayin da wutar rikici ke ci a garin. Sai dai wannan ba haka ba ne.

Da muka yi binciken tushen hoton a Google, mun gano cewa an dauki bidiyon ne a watan Fabrairu na 2021 daga cikin mota, a lardin Benina da ke Benghazi a kasar Libya.

Labarin tserewar zaki a Sudan karya ne

Ana cakuda hotunan Sudan da na Habasha

Wannan sakon na shafin Twitter ya nuna wai sojojin Sudan suna janyewa daga Habasha sakamakon rikicin da ake a kasarsu a watan Afrilu. Wannan ma labarin kanzon kurege ne.

Hoton farko an samo shi ne a shafin intanet na Getty Images ranar 3 ga watan Mayu na shekarar 2015, sai kuma a shafin jaridar Sudan Tribune a nan ranar 19 ga watan Maris na 2022.

A nan kuma an wallafa shi ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2023, a nan kuma an wallafa shi ranar 6 ga watan Agusta shekarar 2022.

Hotunan Habasha ne, ba na Sudan ba /Hoto: Screengrab

Wani bidiyon da ke yawo kuma a Twitter wanda ake ikirarin ya nuna sojin Sudan sun fara kashe fararen hula, ya tabbata na karya ne.

A yankin Gambela na Habasha ne ba a Sudan ba abin ya faru, a shekarar 2022. Fim din ya kunshi duka shaidun da muke bukata don kammala bincikenmu.

Daya daga cikin mayakan a bidiyon an nuno shi yana dauke da robar ruwa wacce kamfanin "Mogle Bottled Water Manufacturing" suka yi, wanda yake samar da ruwan roba mai suna "One Water", kuma a garin Sebeta yake, a kudu maso yammacin Addis Ababa, a Habasha.

Sannan ana iya ganin tutar Habasha ta yankin Gambella a inifam daga saman hagu na kirjinsa lokacin da ya shigo bidiyon.

Kenan babu abin da ya hada rikicin Sudan da wannan bidiyon.

An yi nazarin tutar kasa da robar ruwa don bin diddigin labarin karya game da yakin Sudan

Wai an ga rukunin helikwaftoci suna tashi

Akwai masu ikirari a wani bidiyon mai nuna wai jirage masu saukar ungulu na sojoji suna tashi a sararin samaniyar Sudan yayin wannan rikici, amma duka karya ne.

Duk da an yi amfani da jiragen yaki a wannan rikici tsakanin soji da ‘yan tawayen RSF, shi dai wannan bidiyon ba daga rikicin ba ne.

An wallafa bidiyon ne a tashar labaran Larabci ta Arab news ranar farko na bikin tunawa da sojin Sudan karo na 68 a shekarar 2022.

Hakan ya faru ne a wajen wani fareti, amma sai ake yada cewa a lokacin wannan rikicin abin ya faru.

Ana sauya wa labarai tarihi da kwanan wata /Hoto: Creengrab

Kwararru sun nemi masu amfani da shafukan sada zumunta da a kullum su tantance bayanan da suke gani kafin amfani da su.

Wannan ya wajaba saboda hadarin yada labaran karya musamman a yanayi mai sarkakiya irin na rikicin Sudan.

TRT Afrika