Max Air ta ce ma'aikatanta sun tunkari lamarin yadda ya dace kuma sun tabbatar da kwashe mutane da ma'akata daga jirgin yadda ya kamata:Hoto/Facebook/MaxAir

Fasinjoji 59 daga birnin Legas zuwa Kano sun tsallake rijiya da baya bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa a birnin Kano inda ya zame daga kan titin jirgi bayan tayarsa ta fashe.

Kamfanin dillancin labaran Turkiyya (AA) ya ambato wasu fasinjojin jirgin suna cewa jirgin ya rasa ɗaya daga cikin ababen saukarsa ne a lokacin da ya zo sauka ranar Talata da daddare.

Manajan Kamfanin Max Air a Kano, Bello Ramadan ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce babu wanda ya rasu a cikin matafiyan.

Kuma kamfanin jiragen saman Max Air ya ce za a rufe titin jirgin saman filin saukar jirgi na Mallam Aminu Kano na wucin-gadi zuwa lokacin da aka kammala bincike kan lamarin.

Lamarin dai ya faru da misalin ƙarfe 10.57 na dare a lokacin da jirgin ya isa filin jirgin saman Mallam Aminu Kano daga filin jirgin Murtala Mohammed na Legas.

AA