Daga Abdulwasiu Hassan
Victor Sunday Mutawal na daga cikin mutanen da suka kubuta daga hare-haren da 'yan bindiga suka kai gabanin bikin Kirsimeti a Jihar Filato da ke tsakiyar Nijeriya wadanda suka yi sanadin mutuwar kusan mutum 200.
Ya ce kwatsam aka kai musu hari a tsakiyar bukukuwan karshen shekara yanayin da ya sa mutane suka kasa kare kansu.
Victor, wanda dan asalin kauyen Gawarza Mongor da ke karamar hukumar Bokkos, ya shaida wa TRT Afrika cewa, "Ba na gida a lokacin da suka kai hari, ina cikin garin Jos a daren. "Sun kashe kusan mutane goma daga cikin dangin matata, ciki har da surukina da kuma dansa."
Bayan Victor ya sake kira da safiyar ranar Kirsimeti sai aka shaida masa cewa an sake kai hari karo na biyu, baya ga kisan jama'a da kuma garkuwa da wasu, maharan sun kona gidaje da dama.
“Mun shirya jana’izar mutanen da aka kashe a ranar 24 ga watan Disamba, muna tunanin shi ke nan sun kare,” in ji Monday Kassah, shugaban karamar hukumar Bokkos. " A jajibirin ranar Kirsimeti kuma aka sake shirya kai wani harin a karo na biyu a kauyuka sama da 21."
Daga cikin wadanda suka tsira daga hare-haren, mutum 50 ne da har yanzu suke kwance a asibiti suna fama da raunuka daban-daban, kama daga raunin da suka samu na harbin bindiga zuwa saran adduna.
Gwamnan jihar ya ayyana zaman makoki na mako guda, tun daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa ga 8 na watan ''a matsayin karramawa ga mamatan''.
A wannan lokaci na zaman makoki, za a sauke tutoci , in ji Gwamna Caleb Mutfwang bayan wata ganawa da ya yi da shugabannin al'umma daban-daban a jihar.
“Ina kira ga daukacin ‘yan kasa da su yi amfani da wadannan ranaku wajen gudanar da addu’o’i sosai don neman taimakon Allah Madaukakin Sarki wajen kare yankunanmu daga miyagu da suka taso mana,” inji Gwamnan.
Zargi
Duk da cewa babu wanda ya dauki alhakin kai hare-haren kuma har yanzu jami'an tsaro ba su fitar da sanarwa da ke zargin wata kungiyar ce ke da alhakin kai hare-haren ba, amma wadanda suka tsira sun yi imanin cewa makiyaya ne suka kai harin.
Victor ya ambato wasu da suka tsira suna fada masa cewa maharan makiyaya ne. NIjeriya dai na fuskantar kalubalen tsaro daban-daban da suka hada da rikice-rikicen kabilanci da tashe-tashen hankula ta hanyar yin garkuwa da mutane.
Jihar Filato ta sha fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini fiye da shekaru ashirin kawo yanzu da kuma rikicin manoma da makiyaya.
A shekarar 2004, sai da tsohon shugaban Nijeriya na lokacin Olusegun Obasanjo ya kafa dokar ta-baci a jihar tare da nada gwamnan riko a yayin da rikicin kabilanci ya tsananta a jihar.
Ko bayan an dawo da zababbiyar gwamnatin jihar, an ci gaba da fadace-fadace tare da kai hare-hare a jihar Filato.
Tashe-tashen hankula
Duk da kokarin da gwamnati ke yi na dikile hanyoyin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, har yanzu ba a daina zubar da jini ba.
Al’ummomin da hare-haren suka shafa kai tsaye kafin bikin Kirsimeti sun kaurace wa kauyukansu saboda fargabar kada 'yan bindiga su sake kai musu wani harin.
"A halin yanzu, lamarin ya kai ga babu wanda ke zaune a ƙauyen da na fito, sai wasu matasa da suka yanke shawarar zama don kula da gidajensu. Mata da yara duk sun tafi," kamar yadda Victor ya shaida wa TRT Afrika, yana mai kari da cewa "Haka lamarin yake a kauyen su matata."
Jami'ai sun bayyana cewa an sake kai wa wadanda suka yi kokarin komawa kauyukansu hari.
“Ko a yanzu da nake wannan magana da ku, al’ummar Hurum na karamar hukumar Barkin Ladi suna fuskantar wannan kalubale,” a cewar shugaban karamar hukumar Danjuma Dakil.
"A da sun shirya yin kasadar komawa asalin inda suka fito, inda suka shirya daukar fansa, amma maharan suka sake dawo musu cikin tsakar dare, inda suka kona gidaje da wuraren ibada, tare da yin awon gaba da kayayyankin abinci da suka noma kamar dankali."
Dakil ya yi imanin cewa mutanen kauyen ba za su iya komawa garuruwansu da zama cikin kwanciyar hankali ba "sai dai idan hukumomi sun dauki matakai masu tsauri".
Kwamandan rundunar sojin kasar da ke kula da yankin, Abdulsalam Abubakar, ya tabbatar wa al’ummar yankin cewa “ba za mu huta ba har sai mun gurfanar da duk wadanda ke da hannu a wannan aika-aika," in ji shi.
Laluben mafita
Kawo yanzu mahukunta a yankin sun ce ba su san musabbabin hare-haren ba, amma hanya daya a hukumance ita ce, sai kowa ya tashi tsaye tare da hada hannu don hana sake kai duk wani hari kan al’umma.
"Muna kan tattaunawa, yanzu haka muna bin diddigin abin da ya haifar da tashin hankalin, sai dai ba mu kai ga samun wani abu da ya tunzura faruwar hakan ba, a matsayinmu na gwamnati, burinmu shi ne mu maido da zaman lafiya," kamar yadda Monday Kassah ya shaida wa TRT Afrika.
Shugaban karamar hukumar Barkin Ladi, Dakil, ya ce karamar hukumar ta dora alhaki kan ''manyan jami’ai gwamnati don su umarci jami'an soji wajen yin abin da ya kamata."
Tuni dai shugaba Bola Tinubu ya umarci rundunar sojin kasar da su gano tare da kama maharan da suka aikata wannan ta'asa ta kisan gilla tare da tabbatar da cewa an hukunta su.
Ga al'ummomin da suka rasa matsugunansu, ana ci gaba da jiran ranar da za su koma gida ba tare da fargabar sake kai musu wani harin ba.