DSS ta bukaci 'yan Nijeeriya su sanya ido sosai yayin bukukuwan sallar layya./Hoto:OTHER

Rundunar tsaro ta DDS a Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe wani fitaccen dan bindiga wanda ya taba tserewa daga kurkuku, Kabir Bala wanda aka fi sani da Okwo.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter da asubahin nan ta ce dakarun nata sun kashe Okwo yayin da suka yi ba-ta-kashi da shi da yaransa a jihar Kogi da ke arewacin kasar.

"A wani samamen hadin-gwiwa da safiyar yau, 22 ga watan Yuni, 2023, dakaru sun kai mamaya maboyar Kabir Bala da aka fi sani Okwo, wanda ya taba fasa gidan yari kuma shahararren dan bindiga a Ejule, karamar hukumar Ofu ta jihar Kogi.

Okwo da 'yan bindigarsa sun yi ba-ta-kashi da bindigogi da dakarunmu abin da ya kai ga kashe shi. Amma sauran sun tsere," in ji sanarwar, wadda kakakin DSS Peter Afunanya ya sanya wa hannu.

Ta kara da cewa dakarunta sun kuma kwato makamai da suka hada da bindiga uku kirar AK47 wadanda aka makare da harsasai, makamai shida kirar gida da wayoyin salula biyu da kuma layu.

Shirin kai hare-hare ranar sallar layya

DSS ta kara da cewa wasu rahotanni sun nuna mata cewa wasu na kitsa kai hare-hare yayin bukukuwan sallar layya.

"A nata bangaren, DSS tana kira da a sanya ido sosai gabanin sallar layya, musaman bayan rahotanni sun nuna cea ana shirin kai hari a wuraren ibada da na shakatawa kafin da kuma yayin bukukuwan sallah," in ji Afunanya.

Hakan ya fito fili ne sakamakon abubuwan fashewar da aka kama daga hannun 'yan ta'adda, in ji sanarwar.

Kazalika DSS ta ce dakarunta sun kai samame a jihar Nasarawa kan fitaccen dan bindigar nan Abubakar Muhammad wanda ake kira Abu Direba.

Ta ce yayin samamen, an kwato makamai da alburusai da motoci.

TRT Afrika