Hukumar tsaro ta DSS ta bayyana cewa ta bankado yunkurin da wasu manyan masu ruwa da tsaki a fagen siyasa suke yi na ganin an kafa gwamnatin rikon kwarya a Nijeriya.
Wata sanarwa da kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya fitar ranar Laraba ta ce yunkurin wadannan mutane ba hankula kawai zai tayar ba, har ma da yin watsi da kundin tsarin mulki da kuma jefa kasar cikin rikici.
“Wannan abu take doka ne kuma ba za a taba yarda da shi a kasar da ke bin tsarin dimokradiyya ba da kuma tayar da hankalin ‘yan Nijeriya,” in ji sanarwar.
DSS ta fitar da sanarwar ne makonni kadan bayan kammala manyan zabukan Nijeriya na shugaban kasa da gwamnoni da ‘yan majalisun tarayya da na jihohi.
Jam’iyya mai ci ta APC ce ta yi nasara a zaben shugaban kasa, kuma tuni hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, INEC ta bai wa dan takarar da ya yi nasara Bola Ahmed Tinubu takardar shaidar cin zaben.
Sai dai manyan jam'iyyun adawa biyu na PDP da LP suka yi watsi da sakamakon tare da shigar da kara a kotu.
Sanarwar DSS ta ce “Wannan abu yana zuwa ne bayan kammala zabuka lami lafiya a mafi yawan sassan kasar.
“Masu kitsa wannan shiri a wajen tarukansu, sun yi nazari kan hanyoyi daban-daban da suka hada da daukar nauyin gagaruman zanga-zanga a manyan birane don a sanya dokar ta baci.
“Daya hanyar kuma ita ce don a samu hukuncin kotu da zai hana rantsar da sababbin shugabannin da aka zaba ciki har da ‘yan majalisun dokokin tarayya da na jihohi,” in ji DSS.
Hukumar tsaro ta farin kayan ta ce a don haka tana jaddada goyon bayanta ga shugaban kasa kan aniyarsa ta mika mulki cikin lumana kuma za ta tabbatar da hakan.
“Za mu hada hannu da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cewa an mika mulki salin alin ranar 29 ga watan Mayun 2023.
DSS ta yi kakkausan gargadi ga masu son rusa dimokradiyya a kasar da su janye “munanan aniyoyinsu.”
Ta kuma yi kira ga hukumomin shari’a da kafafen yada labarai da kungiyoyin fararen hula da su sa ido tare da yin taka tsantsan wajen gujewa amfani da su don rusa zaman lafiyar Nijeriya.