Gwamnatin Kaduna da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta tabbatar da bullar cutar makarau a kananan hukumomin Kafanchan da Jema’a na jihar.
Ma'aikatar lafiya ta jihar ce ta ba da sanarwa hakan a ranar Alhamis 20 ga watan Yulin shekarar 2023.
Sanarwar ta ce an samu tabbaci kan bullar cutar bayan rahotannin da aka samu na mutuwar wasu yara wadanda ke zama a yankunan da lamarin ya shafa.
Kazalika wasu mazauna unguwannin Takau da Kafanchan A da Kafanchan B sun nuna alamu na kamuwa da cutar wadanda suka hada da rashin iya numfashi da kyau da zazzabi mai zafi da tari da samun raunin gaba daya da jin zafi a makogwaro da kuma kumburin wuya.
Tuni dai Gwamnan Kaduna Uba Sani ya ba da umarni ga ma’aikatar lafiya ta jihar da ta gaggauta aikewa da tawagarta domin gudanar da bincike kan lamarin da kuma daukar matakin gaggawa a wauraren da aka tabbatar da bullar cutar.
A farkon watan nan hukumar dakile yaduwar cututtuka a Nijeriya NCDC ta tabbatar da barkewar cutar makarau a kasar inda ta ce ya zuwa lokacin mutum 80 ne suka mutu.
NCDC ta ce ya zuwa ranar 30 ga watan Yuni a kalla mutum 798 ne suka kamu da cutar.