Gidauniyar Aliko Dangote Foundation ta attajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote na Nijeriya, ta gudanar da aikin raba buhunan shinkafa ga ƙungiyoyin agaji guda 48 a birnin Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya.
Wannan ya zo ne ƙarƙashin wani shirin gidauniyar mai taken Tallafin Abinci na Ƙasa, inda aka raba dubban buhunan shinkafa ga marasa galihu da gidajen marayu a Abuja.
A cewar kakakin kamfanin, Anthony Chiejina, manufar shirin shi ne cigaba da sadaukarwar gidauniyar Dangote na tallafa wa gwamnatin Nijeriya wajen rage matsin tattalin arziƙi a ƙasar.
Mr. Chiejina ya bayyana cewa bayan an ƙaddamar da shirin raba kayan abincin a Kano da Lagos, gidauniyar ta fara raba buhuna miliyan ɗaya na shinkafa a duka ƙananan hukumomin Nijeriya a watan da ya wuce.
Rabon da ake yi a Abuja yana ƙarƙashin kulawar ƙungiyar 1Ummah Foundation, wadda Mrs. Azeeza Hassan-Jibril ke jagoranta. Da take magana da 'yan jarida, Mrs Jibril ta ambato sauran ƙungiyoyin da ke taimaka wa Gidauniyar Dangote kan aikin.
Ƙungiyoyin sun haɗa da Hope for survival Children’s Home Gishiri, Child to Child Charity Foundation, Gajiya Charity Foundation, Mission for Education, Social and Health (MESH), JADAFIA Group, da kuma Network of Women with Disabilities (NWD).
Sauran su ne Dagam Pilame Community Association, Eeqra Foundation/Orphanage, Leprosarium-Yangoji, Support our Toops (SOT) Foundation for Widows, Karmajiji Disabled Colony, Bimbola Nutrition and Health Foundation, NASFAT Foundation, da JIBWIS Group, da sauransu.
Da yake mai da jawabi, wakilin ƙungiyar Bimbola Nutrition and Health Foundation, Mr. Femi Akosile ya ce: “Muna amfani da wannan dama don gode wa Gidauniyar Aliko Dangote Foundation da ta ba mu buhuna shinkafa mai kilo 10 don raba wa marasa galihu da gajiyayyu“.
Ya ƙara da cewa sun raba shinkafar da iyalai da ɗaiɗaikun mutane da ke da matsalar abinci. Ya kuma ce haɗin gwiwarsu da gidauniyar na ta burin kawo sauyi a al'umma da sauƙaƙa rayuwarsu.