A yau Juma’a ake sa ran daliban Nijeriya da aka kwaso daga Sudan za su isa Abuja, babban birnin kasar.
An soma kwaso daliban ne ranar Alhamis bayan sun kwashe kwanaki suka korafi game da mawuyacin halin da suka shiga sakamakon rikicin da ya barke a Sudan tsakanin sojojin kasar da dakarun runduna ta musamman da ba ta gwamnati ba mai suna Rapid Response Force, RSF.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya, NEMA, ta wallafa sako a shafinta na intanet cewa “ana sa ran kashin farko na kusan ‘yan Nijeriya 1600 da gwamnatin tarayya ta hanyar NEMA ta kwaso daga Sudan” su isa Abuja a yau Juma’a.
“Tawagar motoci 13 da ke dauke da kashin farko na wadanda aka kwaso daga Khartoum na kasar Sudan tana tafiya zuwa yankin Aswan na kasar Masar kuma daga nan jirgi zai dauke su zuwa Nijeriya,” in ji NEMA.
Ta kara da cewa tana tattaunawa da kamfanin jiragen sama Air Peace, wanda ya ce zai kwaso daliban don radin kasan da zarar sun isa Aswan.
Tun da farko a ranar Alhamis daliban sun wallafa bidiyoyi a soshiyal midiya inda suka rika korafi kan yadda motocin da suka debo su suka lalace a dokar-daji.
Sai dai a sakon da ta wallafa a shafin Twitter, shugabar hukumar da ke kula da 'yan Nijeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri, ta ce NEMA ta tabbatar mata cewa motocin sun ci gaba da tafiya a kan hanyarsu ta isa Masar.