Ana kwantar da marara lafiya a asibitocin wucin-gadi. / Hoto: Reuters

Cutar amai da gudawa da zazzabin dengue sun yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100 tun daga watan Agusta, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Sudan ranar Asabar.

Ma'aikatar ta ce mutum 1,049 ne suka kamu da kwalara, 73 suka mutu a Khartoum, da jihar Al-Jazira da ke kudancin birnin da kuma jihar Gedaref da ke yammacinsa.

Khartoum ya kasance fagen daga tun watan Afrilu lokacin da yaki ya barke tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF.

Dubban mutane sun tsere daga birnin Khartoum zuwa yankunan da ke da saukin rikici a jihohin Gedaref da Al-Jazira, inda ake fama da karancin ruwa mai tsafta.

Ma'aikatar lafiyar Sudan ta kara da cewa zazzabin dengue wanda sauro ke haddasawa ya barke a jihohi tara inda ya kama mutum 3,316, cikinsu kuma 49 suka mutu.

A Jihar Gedaref, wadda ke kan iyakar kasar da Ethiopia, mutum 2,152 sun harbu da cutar inda mutum 33 suka mutu.

Tun kafin yakin da aka soma a watan Afrilu, harkokin kiwon lafiya a Sudan na fama da dimbin kalubale wajen shawo kan cutukan da kan barke bayan saukar damuna galibi a watan Yuni.

Yanzu lamarin ya kara tabarbarewa ganin cewa an yi luguden wuta a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da dama, sannan likitoci da dama sun tsere daga kasar, kana babu isassun magunguna.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce kashi 70 cikin dari na asibitoci a yankuna da yaki ya fi kamari sun daina aiki.

AFP