Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo ta ce ta fara tattaunawa da Zambia kwana guda bayan da maƙociyarta ta kudancin Afirka ta rufe iyakarsu. Matakin ya toshe babbar hanyar da Congo ke amfani da ita don fitar da Copper zuwa ƙasashen waje, a matsayinta na ƙasa ta biyu a duniya a yawan fitar da ƙarfen Copper.
A ranar Asabar, ministan Kasuwanci na Zambia, Chipoka Mulenga ya sanar da rufe iyakar na wani ɗan lokaci, bayan Congo ta saka haramcin amfani da lemon zaki da barasa da aka shigo da ita, inda ya haifar da zanga-zangar direbobin dakon kaya a garin Kasumbalesa da ke iyakar Zambia.
"An fara tattaunawa tsakanin gwamnatocin Congo da Zambia tun ranar Lahadin nan, don hanzarta sake buɗe ƙofar iyakar tasu," in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Kasuwanci ta Congo ta fitar a ranar Lahadi.
"A awannin da suka biyo baya, ɓangarorin biyu za su haɗu a Lubumbashi da ke Haut-Katanga, don nemo mafita ta ƙarshe game da kasuwancin."
Sanarwa a hukumance
Ministan Kasuwanci na Congo Julien Paluku Kahongya ya fitar da sanarwa a ranar Lahadi, inda yake cewa ma'aikatarsa ta samu sanarwa a hukumance game da taƙaddamar kasuwanci daga Zambia kafin ta sanar da rufe iyakar.
A sanarwar, ya yi dogon bayani game da yarjejeniyar kasuwancin ƙasashen biyu da kuma hanyoyin magance duk wata taƙaddama da ta taso.
"Ya zuwa yanzu babu wata taƙaddama da aka gabatar wa ma'aikatar a rubuce, ko ta hanyar diflomasiyya," in ji shi. "Ma'aikatar ta shirya duba duk wata buƙata da Zambia ta kawo, matuƙar tana ƙunshe cikin yarjejeniyar, wadda ta hana ramuwar gayya."
Congo ce ƙasa ta biyu a duniya a fannin samar da ƙarfen Copper, kuma ta zo ta 3 a 2023 wajen fitar da shi, bayan ta fitar da tan miliyan 2.84.
Zambia hanya ce mai muhimmanci ga Congo, wajen fitar da Copper, inda ake bi ta garin Kasumbalesa a shiga Zambia.