Hukumomi a kasar Zambia sun aika da jami’an soji domin a yi gaggawar ceto akalla mambobin coci takwas wadanda suka bace bayan hatsarin kwale-kwale.
Kwale-kwalen wanda yake dauke da mambobin coci 44 ya jirkice ne a ranar Juma’a a Tafkin Bangweulu da ke Lardin Luapula.
An ceto mutum 28 inda kuma aka tabbatar da cewa 11 sun rasu. Shugabar ‘yan sanda ta lardin Gloria Mulele ta bayyana cewa mambobin cocin na kan hanyarsu ta halartar wani taro na coci wannan iftila’in ya rutsa da su.
“Wadanda suka tsira an garzaya da su asibitin lardin domin duba lafiyarsu,” in ji Mulele. A wata sanarwa, ta bayyana cewa wadanda suka bace a hatsarin na tsakanin shekara biyu ne zuwa 28.
“Igiyar ruwa mai karfi da iska wadanda suka mamaye tafkin suka ja kwale-kwalen ya jirkice sakamakon mai tuka kwale-kwalen ya rasa yadda zai shawo kansa,” kamar yadda ta kara da cewa.
Sai dai cocin a dayan bangaren ta ce bayanan da ta samu na nuna cewa an ceto mutum 29 har da shi mai tuka kwale-kwalen, inda akwai kuma 15 da ba a gani ba.
“Zuwa yanzu, mutum hudun da aka ceto an kai su asibiti, sauran kuma an sallame su,” in ji cocin.
Mai magana da yawun gwamnati a kasar Chushi Kasanda a bayanan baya-baya da ta bayar ta bayyana cewa an gano gawarwaki takwas, akwai kuma takwas da ba a gani ba.
“Cikin kaduwa da bakin ciki shugaban kasa ya samu labarin hatsarin kwale-kwale wanda ke dauke da mawakan cocin Seventh Day Adventist guda 44 wanda ya yi hatsari a Bangweulu.
“Zafin rasa rayukan matasa da dama a iftila’i daya mai girma irin wannan yana da wuyar juriya,” kamar yadda Kasanda ta kara da cewa.
Ta bayyana cewa tuni aka aika da sojojin ruwa domin taimakawa wurin ganowa da kuma aikin ceto inda ta kara da cewa Shugaba Hakainde Hichilema ya bayar da umarni ga hukumomin gwamnati da su tanadi akwatunan gawarwaki da abinci domin tallafa wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu domin rage nauyi ga coci da kuma iyalan.