Kusan mutum miliyan uku ne suka gudu daga Sudan bayan watanni 18 ana gwabza yaki, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta fada, inda a makon farko na watan Oktoba mutum 25,000 suka gudu zuwa Chadi.
Mamadou Dian Balde, jami'in MDD na shiyya da ke Sudan, ya bayyana cewa nan da makonni kadan masu zuwa za a haura mutum miliyan uku.
Yadda adadin ya doshi miliyan uku na bayyana irin munanar da rikicin ya yi, ya fadi haka a wata tattaunawa a ranar Talata a yayin da ya ziyarci Geneva a makon nan.
Tun watan Afrilun 2023 rikici ya balle tsakanin rundunar sojin Sudan karkashin Abdel Fatah al-Burhan da mayakan RSF karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Dagalo.
Rikicin ya yi ajalin dubban mutane inda kimanin mutum miliyan 26 ke fuskantar barazanar karancin abinci, inda aka ayyana fada wa halin yunwa a Sansanin Zamzam da ke yankin Darfur na Yammacin Sudan.
An tirsasa wa mutum miliyan 11.3 guduwa, ciki har da miliyan 2.95 du suka gudu daga kasar, kamar yadda alkaluman baya-bayan nan daga UNHCR suka bayyana.
Rikici ya munana
Rikici ya munana da tsananta a yankin Darfur, mutane 25,000 - kashi 80 mata da yara kanana - sun tsallaka zuwa Chadi a makon farko na watan Oktoba.
Kuma sama da mutum 20,270 ne suka gudu zuwa Chadi daga Sudan a watan Satumba baki daya.
Chadi ta karbi bakuncin masu neman mafaka daga Sudan 681,944 - sama da kowacce kasa.
Sai dai kuma, ta kasance daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya, inda ta rasa kayan more rayuwa don karbar wannan adadi na 'yan gudun hijira, in ji Balde, yayin da yake karin haske kan karamcin da 'yan kasar Chadi suka nuna na karbar masu gudun hijirar.
"A lokacin da muka ga 25.000 na zuwa. mun ce suna da yawa sosai.," in ji shi.
Ya yi kira da a bayar da gwaggwaban tallafi daga masu tallafawa na kasa da kasa.
Majalisar Dinkin Duniya na neman taimakon dala biliyan 1.51 don taimaka wa 'yan gudun hijirar Sudan da jama'ar da suka karbe su nan da shekara daya, kuma kashi 27 na wannan kudi kawai aka iya amu.
"Ba za su isa ba, saboda adadn 'yan gudun hijirar na ta daduwa," in ji Balde, wanda ya taba zama jami'in UNHCR a yankin Kusurwar Afirka da yankin Tafkin Chadi.
Balde ya ce yana tsammanin "cikin bakin ciki nan da wasu 'yan makonni da za su zo, za a samu karin masu neman mafaka a Chadi," saboda rikicin da ke ruruwa a Darfur da kuma raguwar ruwan sama a yankin.
Karancin kayan agaji
Tare da yanayin rani da aka shiga, MDD na fatan samun damar kai kayan agaji zuwa Sudan - idan bangarorin da ke nrikici suka bayar da damar hakan.
An kasa cimma matsaya a tattaunawar da aka yi da dama don kawo karshen rikicin.
A karshen watan Agusta, bayan tattaunawar da aka yi a Geneva karkashin Amurka, bangarorin biyu sun yi alkawarin bayar da cikakkiyar damar kai kayan agajin jinkai ga mabukata.
"Wannan ya taimaka wajen kubutar da rayuka," amma "ba dukkan alkawarukan aka cika ba" - har yanzu ba a iya kai kayan taimako yadda ya kamata, in ji Balde.
A Geneva wajen taron zartarwa na UNHCR, ya jagoranci tattaunaw akan Sudan, inda a nan ma ya nemi da a tallafa wa jama'ar Sudan da ke gudun hijira da ayyukan yi ta yadda za a rage nauyin dogara kan taimakon jin kai.
"Muna kira ga masu kawo cigaba da su bayar da taimako" irin wannan taimako, zai taimaka sosai, inda ya kuma bayyana bukatar zaman lafiya a Sudan.
Balde ya yi gargadin cewa zai zama "babban kuskure" idan aka yi tunanin cewar kwarar wadanda aka raba da matsugunansu za ta tsaya a Sudan da yankin kawai.