Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun ayyana Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban kasar, a cewar wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar.
"Kowa ya amince da Janar Oligui Nguema Brice a matsayin shugaban Kwamitin Mika mulki da Dawo da Hukumomi," a cewar wani soja da ya karanta jawabi a gidan talabijin na Gabon 24, zagaye da manyan sojoji.
Wane ne Brice Oligui Nguema?
Nguema ya fito ne daga lardin Haut-Ogooue da ke kudu maso gabashin Gabon, wanda ke da iyaka da Jamhuriyar Kongo.
Shi ma Bongo daga wannan lardin ya fito.
Nguema, ɗa ne ga wani tsohon soja, kuma ya yi karatu a makarantar sojoji ta Royal Military Academy of Meknes a kasar Maroko.
Brice Oligui Nguema shi ne shugaban runduna ta musamman da ke tsaron fadar shugaban kasar Gabon.
Yana daya daga cikin sojojin da ke tsaron lafiyar Bongo kafin a kara masa girma zuwa mukamin shugaban runduna ta musamman da ke tsaron fadar shugaban kasar Gabon a 2009.
Hasalima an kara masa girma ne bayan an cire ɗan uwan Bongo daga kan mukamin, a watan Oktoba na shekarar ta 2009.
Jim kadan bayan an nada shi kan mukamin, Nguema ya kaddamar da wani shiri mai taken "tsarkake zukata" da zummar kawar da mutanen da ake zargi da wawushe kudin kasar.
Labari mai alaka: Ali Bongo Ondimba ya sake yin nasara a zaben shugaban kasar Gabon
Wannan juyin mulki na Gabon shi ne na takwas da aka yi a Yammaci da Tsakiyar Afirka tun shekarar 2020. Kazalika ya kawo karshen mulkin shekara 56 da zuriyar Bongo ta kwashe tana yi a kasar.
Sojoji sun yi juyin mulkin ne jim kadan bayan hukumar zaben kasar ta sanar Ali Bongo a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Asabar inda ya samu kashi 64.27 na kuri'un da aka kada.
Bongo ya nemi agajin abokansa a fadin duniya
Tun da fari, shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya bayyana a wani bidiyo inda ya yi kira ga "abokanmu" su yi "magana" bayan sojoji sun kifar da gwamnatinsa.
"Ina tura sako ga dukkan abokanmu da ke fadin duniya su yi magana (…) mutane a nan sun tsare ni da iyalaina," in ji shi, fuskarsa cike da damuwa, a bidiyon da aka watsa a shafukan intanet.
Kamfanin BTP Advisors da ke gudanar da harkokin sadarwa wanda ya yi aiki kut da kut da iyalan Bongo ya tabbatar da sahihancin bidiyon.
Sai dai Malika Bongo Ondimba, 'yar shugaban kasar da aka hambarar, ta taya Janar Nguema murnar yin juyin mulki a sako sako da ta wallafa a shafinta na X, wanda a baya ake kira Twitter.
Ta yi takarar zama 'yar majalisar dokokin kasar a zaben da aka gudanar ranar Asabar.