Barazanar ambaliyar ruwa a Afirka/ AA

Masu yawan shakatawa 334,552, yawanci daga Turai ne suka je kasar a shekarar 2022, yawan da ya haura na shekarar 2021 kamar yadda kididdigar sashen kula da masu bude ido ta nuna.

Amma yanzu hauhawar teku na barazana ga tsibirin.

Kwamitin hadakar gwamnati a kan sauyin yanayi ya yi hasashen cewa hauhawar teku za ta kai tsakanin inci 8 zuwa 34 a shekarar 2100. Kwamitin ya yi bayanin cewa hauhawar za ta faru ne saboda "narkewar kankara da fadadar teku saboda yanayin zafi."

Tsibirin 115 da a nan ne wajen shakatawa na Seychelles yake ya kai har zuwa sashen Tekun India, kuma kowane bangare yana da nasa abin sha'awar da ke jawo hankalin masu yawon bude ido.

A lokacin da wasu ke zuwa domin ninkaya a teku da wankan turbaya a farar kasa, wasu suna zuwa ne domin wasannin da ake yi a cikin ruwa kamar tseren kankara da ninkaya zuwa karkashin teku.

Yanzu babban tashin hankalin mutanen kasar su 98,000 shi ne yiwuwar nutsewar tsibirin nasu.

Wani masunci a tekun Beau Vallon da ke tsibirin Mahe mai suna James ya bayyana wa TRT Afirka cewa sun lura tekun na ta kara fadada yana cinye gabarsa kuma wajen kamun kifi na raguwa.

"A kusa da teku aka haife mu, a nan muka taso, babu abin da muka sani sai teku," in ji shi, sannan ya kara da cewa, "A da can akwai kifaye sosai, amma yanzu suna raguwa.

Kifin da ake samu ya ragu sosai idan ka kwatanta da abin da ake samu a baya." Ya yi bayanin cewa yanzu wasu bishiyoyi da a da suke fitowa a bakin tekun duk sun bace.

A kusa da bakin tekun na Beau Vallon akwai katangar gabar teku da gwamnati ta gina domin kiyaye ballewar teku ko wasu matsalolin da sauye-sauyen yanayi za su iya jawowa.

A tsibirin Mahe da James ya rayu na sama da shekara 50 ne akwai birnin Victoria, Babban Birnin Seychelles, inda a nan ne akwai kusan kashi 90 na mutanen Seychelles din suke.

A birnin, wanda tudu ne da yake da tsawon mita 2.5 a sama da teku ne akwai muhimman gine-ginen gwamnati irinsu filin jirgin sama da ma'adinan man fetur da hukumar bayar da agajin gaggawa.

TRT Afirka ta tattauna da Dokta Nirmal Shah, Babban Jami'in Gudanarwa na Nature Seychelles, wadda kungiya ce mai kula da muhalli.

Ya ce duk wani dan Seychelles ya san sakamakon dumamar teku da guguwa da tsawa.

"Za mu iya kwashe duk muhimman gine-ginen daga kusa da teku, inda da yawansu suke mu mayar da su wasu wuraren, sai dai hakan na bukatar makudan kudade," in ji Dokta Shah.

Ya kara da cewa, "Mutane da dama ba su fahimci cewa akwai barazana da muke fuskanta ba.”

Magance matsalar

Wasu kasashe da suke kananan tsibirai a yankin Gaashin Afirka ma suna fuskantar irin wadannan matsalolin na sauyin yanayi kamar su Cave Verde da Mauritius da Reunion da Sao Tome and Principe da Comoros.

A taron sauyin yanayi na shekarar 2022 da aka yi a Masar (COP 27), hadakar kananan tsibirin kasashe sun yaba da assasa 'Asusun Asara da Barna' wanda a cewarsu wata hanya ce ta tabbatar da adalci a batun sauyin yanayi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an assasa asusun ne 'Domin bayar da tallafin kudi ga kasashen da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayi."

Dokta Shah ya bayyana wa TRT Afirka cewa wannan asusun tun tuni dama ake bukatarsa, sai dai a cewarsa duk da cewa asusun yana da muhimmanci ga kananan kasashen, amma har yanzu babu gamsasshen bayani kan yadda za a samu kudade daga asusun da kuma yadda za a kula da shi.

"Maganar gaskiya wannan shi ake kira alkawarin muzuru. Ba mu san yaya asusun yake ba, kuma nawa ne kudin da za a saka a ciki," in ji shi, sannan ya kara da cewa, "Shin zai zama kamar inshora ne kamar yadda Kungiyar Tarayyar Turai ta fada?

Kuma yawancin kudade daga kamfanoni da sauran masu zaman kansu suna da wahalar samu ga kananan kasashe?"

Ya yi gargadin cewa akwai bukatar mutane su fahinci cewa ko an samu kudaden, akwai abubuwan da ba za a iya gyarawa ba.

"Wannan abu ne da na lura cewa mutane da dama ba su fahimta ba, kamar yadda suke tunanin za mu iya gyara su, kamar wasu muhimman halittun karkashin ruwa. Aikin gama ya gama," in ji Dokta Shah a zantawarsa da TRT Afirka.

“Mun yi asarar kasa, mun yi asarar bakin teku na har abada. Ba zai yiwu mu dawo da wadannan abubuwan ba.

Sannan mun yi rashin hanyar abincinmu domin duk tudun da mutane suke samun damar shuka kayan marmari da ganyayyaki sun yi dandanon gishiri da ba zai yiwu a yi noma ba. Don haka zai yi wahalar gaske a gyara wadannan abubuwa," in ji shi.

Wasu mazauna yankin kamar su masunci James sun cire tsammanin za a dauki wani mataki a game da matsalar.

"Babu wata hanyar da za a magance matsalar. Yanzu babu wani bakin teku da ya rage. Hanya daya tilo ita ce kawai a bar su yadda suke a yanzu," in ji shi.

Masanin muhalli, Dokta Shah, ya yi amannar cewa hanyar da za a magance matsalar tana ta'allaka ne a kan yadda kasashen duniya suka sa hannu wajen rage dumamar yanayin duniya da fitar da sinadarai masu illa ga muhalli.