Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce ba za ta fasa yajin aikin da ta ƙuduri aniyar tsunduma ranar Litinin ba game da buƙatarta wajen gwamnatin ƙasar kan ƙarin albashi mafi ƙaranci ga ma'aikatan ƙasar.
Shugabannin gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC ne suka bayyana haka jim kaɗan bayan sun fito daga taron da suka gudanar ranar Lahadi da daddare da shugaban majalisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilan ƙasar Tajuden Abbas don samun bakin-zaren, wanda da alama bai cim ma wata nasara ba.
“A halin da ake ciki, ba mu da ikon yanjewa daga yajin aikin da za a soma ranar Litinin da safe, za a tafi yajin aikin a yayin da za mu gabatar da roƙon da shugabannin Majalisar Dokokin ƙasar suka yi ga rassanmu daban-daban a kan mu janye yajin aikin” in ji shugaban ƙungiyar masu masana'antu (TUC) Festus Osifo, bayan shi da shugaban ƙungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Joe Ajaero sun fito daga taron.
Ƙungiyoyin Ƙwadagon sun yanke shawarar tafiya yajin aiki ne bayan sun kasa samun matsaya da gwamnatin tarayya kan mafi ƙarancin albashi da kuma buƙatarsu ta neman a janye ƙarin da aka yi na kuɗin lantarki a faɗin ƙasar.
Shugabannin ƙwadagon sun ce ba za su ci gaba da amincewa da N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Nijeriya, musamman ganin cewa ko a hakan ma akasarin gwamnonin jihohi ba sa iya biyan ma'aikata, shekara biyar bayan tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar sabunta albashi hannu.
A taron ƙarshe da ƙungiyoyin ƙwadagon suka yi da gwamnati kafin ayyana tafiya yajin aikin, sun yi fatali da aniyar gwamnati ta biya N60,000 a matsayin mafi ƙaranci albashi a Nijeriya. Duka ƙungiyoyin NLC da TUC sun dage cewa dole ne gwamnati ta riƙa biyan aƙalla N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Masu lura da lamura suna gani yajin aikin zai jefa 'yan Nijeriya cikin ƙarin matsi a yayin da ƙasar na fama da hauhawar farashi mafi girma cikin kusan shekara talatin.