Janar Christopher Musa ya ce duk da yake jami’an tsaro sun yi ƙoƙarinsu a jiyan, to dole sai illahirin ‘yan Nijeriya sun saka hannu sun taya su don a yi nasara . / Hoto:AP

Rundunar sojin Nijeriya ta ce ba za ta zura ido ta bar wasu mutane su lalata ƙasar ba da tayar da tarzoma sakamakon zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagari.

A wani taron manema labarai da Babban Hafsan Rundunar Tsaro Janar Christopher Musa ya yi a ranar Juma’a a a Abuja, ya cean ga irin ɓarnar da ta faru a ranar farko ta zanga-zangar da irin yadda aka lalata wurare, “to me zai faru kenan idan aka ci gaba da hakan na tsawon lokaci, don haka rundunar soji da ma illahirin hukumomin tsaro ba za su tsaya suna kallo a ci gaba da hakan ba.”

Kalaman nasa na zuwa ne a yayin da hukumomin tsaro daban-daban ke ta mayar da martani kan irin abin da ya faru a ranar Alhamis da aka fara zanga-zangar, wadda wasu “ɓata-gari” suka yi amfani da damar wajen sace-sacen kayayyakin gwamnati da na al’umma a jihohi da dama.

Janar Musa ya ce “Ina son na gargaɗi duk wasu kangararru cewa ba za mu naɗe hannu mu saka muku ido ku lalata mana ƙasa ba. Za mu ɗauki mataki cikin ƙwarewa kuma duk wanda muka kama za mu miƙa shi gaban kotu don a hukunta shi.”

Tuni dai wasu jihohin suka saka dokar hana fita da ta taƙaita zirga-zirga don shawo kan lamarin da tuni ya fara rikiɗewa rikici a ranar Alhamis ɗin, inda har aka samu asarar rayuka a wasu wuraren kamar yadda shaidu suka ce.

‘Ku daina ara musu murya’

A yayin da yake gode wa manema labarai kan ƙoƙarinsu, Janar Musa ya yi kira ga ‘yan jaridar da su daina kambama labarin zanga-zangar don hakan na ƙara wa masu yin ta zama.

“Na lura a jiya dukkan kafafen watsa labarai sun mayar da hankali kacokan kan lamarin. Wanna abu ba babban zaɓe ba ne, kar ku yi ta yaɗa abin ta yadda za su gani saboda wasunsu dama suna neman damar da za a gan su a talabijin.

“Ina tabbatar muku cewa mu ne za mu yi nasara kuma mun ma yi nasara don tuni mun ga yadda wasu jihohin suka dakatar da ita ta hanyar sanya dokar ta ɓaci,” ya ce.

Da aka tambaye shi kan yadda a wasu wuraren ba a ga jami’an tsaro ba, sai Babban Hafsan Rundunar Tsaron ya ce “jami’an tsaro ba za su iya kasancewa a dukkan ko ina a fadin ƙasar ba. Kun san Nijeriya na da girman da ya kai murabba’in kilomita miliyan ɗaya, don haka ba a bu ne mai sauƙi a saka tsaro a ko ina ba.”

Sai dai ya ce duk da yake jami’an tsaro sun yi ƙoƙarinsu a jiyan, to dole sai illahirin ‘yan Nijeriya sun saka hannu sun taya su don a yi nasara a kuma hana ɓata-gari amfani da damar wajen yin son ransu.

TRT Afrika