Muna sane da yadda wasu bata gari ke yunkurin kawo rudani a cikin shugabancin jam'iyyar APC in ji sanarwar Yahaya Bello. Yahaya Bello Facebook

Tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya ce yana biyayya ga jagorancin Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta Nijeriya.

Sakon Yahaya Bello na zuwa ne a lokacin da ake ta yaɗa batun cewa yana neman takarar jam’iyyar kuma za a yi babban taro na zaɓen sabon shugaban APC nan ba da jimawa ba.

A sanarwar da ofishin watsa labaran Yahaya Bello ya fitar a ranar Talata da maraice, ya ce “Muna sane da yadda wasu bata-gari ke yunkurin kawo rudani a cikin shugabancin jam'iyyar APC. Wannan aiki ne na wasu jiga-jigan 'yan adawa da wasu masu zagon kasa a cikin jam'iyyarmu.”

A makon nan an yi ta yaɗa batun cewa nan ba da jimawa ba APC za ta yi taron zaben sabon shugaban jam’iyya, kuma Yahaya Bello za a bai wa shugabancin, inda har ake wallafa fastocinsa da nufin hakan.

Sai dai sanarwar ta ce “A wani bangare na zancen da ake watsawa har da yada hotunan yakin neman zabe dauke da hoton Alhaji Yahaya Bello, CON, tsohon gwamnan jihar Kogi, ana cewa ya fito takarar shugaban jam'iyyar APC na kasa. Labarin ƙage ne, ƙarya kuma ya kamata a yi watsi da shi.”

Yahaya Bello, wanda ya sauka daga mukamin gwamnan Kogi a makon da ya wuce bayan ƙarewar wa'adinsa, ya ce jam’iyyarsu ta APC ba ta da wani shiri na gudanar da babban taro ko zaben sabon shugaba, don haka babu wata fa’ida ta yada fastocin neman ko wane irin shugabanci a jam’iyya.

“Alhaji Yahaya Bello bai bai wa kowa izinin yada wata fosta a madadinsa ba domin ya kasance mai biyayya ga jam’iyya mai kishin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, mai girma Gwamna Dr Abdullahi Ganduje.”

Dama an daɗe ana yaɗa batun cewa shugabancin jam'iyyar APC na shiyyar Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ne a wannan karon, amma babu wani tabbacin hakan da aka ji daga wajen jam'iyyar.

A ƙarshe sanarwar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da “ƙaryar da jama’a ke ta yaɗawa da fastoci don haifar da rashin gaskiya.”

TRT Afrika