Elrufai ya ce zai mayar da hankali a fannin 'yan kasuwa masu zaman kansu. Hoto/@GovKaduna

Gwamnan Jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya, Nasir Elrufai, ya musanta rade-radin da ake yi cewa zai zama shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a gwamnatin zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana haka ne a Gombe ranar Asabar yayin da ya ziyarci Jihar don kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya gudanar.

Elrufai ya ce idan ya sauka daga mulki a karshen watan Mayu zai mayar da hankali kan fannin 'yan kasuwa masu zaman kansu.

"Ban tattauna da zababben shugaban kasa (a kan wannan batu ba) kuma ba na son jita-jita. Na karanta a jaridu cewa za a ba ni wasu mukamai. Ina son kasata da kuma ci gabanta. Amma ba sai na yi aiki a cikin gwamnati ba.

“Akwai hanya fiye da daya da za ka taimaka wajen cigaban kasar nan kuma ba zan taba daina aiki don cigaban Nijeriya ba. Zan kasance a bangaren 'yan kasuwa masu zaman kansu, ba shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ba."

Gwamna Elrufai ya ce zai yi hutu bayan ya sauka daga mulki sannan ya rika ba da shawara ga masu mulki idan suka bukaci hakan daga gare shi.

Gwamnan na Kaduna, wanda a baya ya rike mukamai ciki har da ministan babban birnin tarayya Abuja, yana cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen nasarar jam'iyyar APC da kuma goyon bayan dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu.

Hakan ne ya sa ake ta yada jita-jita a kan yiwuwar nada shi a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

TRT Afrika