Babban Bankin Nijeriya CBN ya nesanta kansa daga wani labari da ake yaɗawa kan cewa yana da niyyar mayar da kimanin dala biliyan 30 da ke asusun ajiyar kuɗaɗen waje na bankunan Nijeriya zuwa naira.
Babban bankin ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar inda ya musanta lamarin tare da cewa ana yaɗa labarin ne domin saka fargaba a zukatan jama’a.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da nairar ke ci gaba da karyewa a kasuwar hada-hadar ƙasashen waje inda har ta kai ga an canja dala ɗaya kan naira 1,500 a ƴan kwanakin nan.
“Wannan zargin ƙarya ce kuma ana yin sa ne domin saka fargaba a kasuwar hada-hadar ƙasashen waje, wadda CBN ke tuƙuru domin daidaitawa, kamar yadda ayyuka na baya-bayan nan da tsare-tsare suka nuna,” in ji babban bankin.
“An yaɗa irin waɗannnan ƙarerayin kan aikin CBN a watannin da suka gabata kuma a bayyane take kan cewa ana so a yi ƙafar ungulu ne ga irin ƙoƙarin da muke yi.
“Muna so mu tabbatar wa jama’a cewa CBN na da aminci kuma ba za ya yi duk wani abu da zai kawo matsala ga kuɗi ko tattalin arziki ba,” in ji babban bankin.
Ko a cikin makon nan sai da aka rufe wasu daga cikin manyan kasuwannin canji na bayan fage da ke Nijeriya domin nuna rashin jin daɗi dangane da karyewar darajar nairar.