Angola za ta sayar da kamfanin mai na biyu mafi girma a Afirka

Angola za ta sayar da kamfanin mai na biyu mafi girma a Afirka

Kamfanin mai na Angola Sonangol da aka samar a 1976, na da yawan ma’aikata kusan 13,000.
Angola na daya daga cikin kasashen duniya mafiya arzikin mai. Photo: Rueters

Gwamnatin Angola ta bayyana shirin da ake da shi na kammala sayar da kamfanin manta mai suna Sonangol.

Kamfanin Sonangol ne kamfanin mai na biyu mafi girma a Afirka, kuma nan da 2026 ake shirin kammala cefanar da shi, kamar yadda Cibiyar Kula da Kadarorin gwamnati ta bayyana a ranar Larabar nan.

Shugabar kamfanin Patricio Vilar ta bayyana cewa za a dauki lokaci mai dan tsawo kafin a kammala cefanar da Sonango saboda yadda yake da girma a duniya.

Sonangol na fitar da albarkatun mai ganga miliyan biyu a kowacce rana.

A ranar Larabar nan a yayin gana wa da manema labarai a Luanda babban birnin Angola, Vilar ya ce “Ba za a kammala cefanar da kamfanin a wannan shekarar ba.

"Amma kuma ana mataki na biyu na ayyukan wanda za a kammala nan da 2026,”

Cibiyar ta bayyana karbar rahoton tantancewa da binciken ayyuka a kamfanin, kuma Vilar ya kara da cewa sai an kammala komai kafin a sayar da Sonango.

Ziyarar gani da ido

A ranar Laraba wakilan Cibiyar sun ziyarci babban ofishin Sonangol “don fahimtar yadda yake gudanar da ayyuka”.

Shugaban Sonangol Sebastiao Martins ya ce gwamnati na ayyukan tacewa da sabunta dokoki domin cefanar da shi.

A shekarar 2021 ne gwamnati ta fara sayar da hannayen jarin kamfanin, inda ta bayyana tana son mallakar kaso 30 ne kawai.

A watan Oktoban 2021, gwamnatin Angola ta ce cefanar da kamfanin Sonangol zai samar da kasuwar mai da ake gogayya da gasa a kasar.

A 1976 ne aka kafa kamfanin Sonangol bayan mayar da Angol mallakin kasa. Kamfanin ne kadai ke da hurumin dillancin danyen mai da iskar gas.

Kamfanin da ke da yawan ma’aikata 13,000, na da kadarori da suka kai darajar dala biliyan 51.5, kamar yadda Cibiyar Sanya Idanu Kan Kadarorin Kasashe ta bayyana.

TRT World