Rashin jituwa tsakanin Nijar da Benin ya samo asali ne bayan Nijar ta ƙi amincewa ta cire takunkumin da ta saka dangane da haramta shigar da kaya daga Benin. / Hoto: Reuters

Nijar ta ci gaba da fitar da man fetur ta Jamhuriyar Benin bayan ƙasashen sun samu matsalar da ta sa aka dakatar da shigar da mai ta hanyar wani sabon bututu da China ta yi aikin shimfiɗawa wanda ya bi ta Benin, kamar yadda kamfanin da ya saka bututun ya sanar a ranar Litinin.

Matsalar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta samo asali ne bayan Nijar ta ƙi amincewa ta ɗage takunkumin da ta saka na hana shigo da kayayyaki daga Benin, wanda hakan ya jawo ƙasar ta Benin wadda ke da arziƙin teku ta mayar da martani ta hanyar toshe fitar da man fetur ta ƙasarta a watan Mayu. A watan Mayu, Nijar ta dakatar da tura mai ta cikin bututun.

Wani jami'in kamfanin na West African Gas Pipeline Company (Wapco), wanda ke kula da bututun man, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba kan cewa wani jirgin ruwa na Aura M ya yi lodin ɗanyen man fetur na Nijar kimanin ganga miliyan ɗaya daga tashar ruwa ta Benin.

Bayanai na bin diddigin jiragen ruwa daga MarineTraffic, mai ba da kididdiga kan teku a duniya, sun nuna cewa an loda jirgin kuma ya tashi daga tashar ruwan Benin da yammacin Talata.

Reuters