Sojojin Sudan da dakarun RSF za su yi zaman "tattaunawa" ta hanyar masu shiga tsakani a maimakon ganawa ido da ido, in ji wakiliyar MDD ta musamman./ Hoto: AFP 

Ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun isa birnin Geneva na ƙasar Switzerland domin tattaunawa kan ''yiwuwar tsagaita wuta a kasar'' wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya da nufin sauƙaƙa ayyukan jin kai da kare fararen hula, in ji mai magana da yawun MDD.

Yaƙin Sudan, wanda ya ɓarke a watan Afrilun 2023 ya tilasta wa mutane kusan miliyan 10 barin matsugunansu, lamarin da ya haddasa barazanar yunwa da rikice-rikice na ƙabilanci waɗanda aka ɗora alhakinsa kan ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF).

Yarjejeniyar da aka ƙulla a birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya tsakanin Sojojin Sudan da dakarun sa kai na RSF wacce Amurka da Saudiyya suka jagoranta a ƙarshen shekarar bara ta wargaje.

''Zaman tattaunawar zai mayar da hankali ne kan lalubo hanyoyin ci gaba da ayyukan jin kai da kuma kare fararen hula ta hanyar tsagaita wuta a ƙasar, kamar yadda Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya buƙata,'' a cewar mai magana da yawun MDD sa'ilin da take amsa tambayoyin kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A cewarta, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Ramtane Lamamra daga Aljeriya ne ya shirya zaman tattaunawar da aka soma a ranar Alhamis.

Sojojin Sudan da dakarun RSF za su yi zaman "tattaunawa" ta hanyar masu shiga tsakani a maimakon ganawa ido da ido, in ji ta.

Jakadiyar Amurka a MDD Linda Thomas-Greenfield ta shaida wa gidan talabijin na CBS cewa, an gayyaci wakilin Amurka na musamman a Sudan Tom Perriello don shi ma yana daga masu zaman tattaunawar a Geneva wanda ya mayar da hankali kan ''yadda za a magance barazanar da ayyukan jin ƙai ke fuskanta da taimaka wa mabuƙata da nemo mafita kan matsalar siyasa domin haɗa ɓangarorin biyun da ke yaƙi da juna wuri guda.''

TRT World