Ana zargin sojojin Chadi da kashe masunta da dama a Nijeriya a yayin da suke yunƙurin kashe masu iƙirarin jihadi, kwanaki kaɗan bayan Boko Haram ta kashe mutum 40 a wani hari da ta kai wani sansanin soji a Chadi, kamar yadda wasu masunta da kuma ‘yan bijilanti suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Sojojin na Chadi sun ƙaddamar da hare-hare ta sama a tsibirin pummelling Tilma da ke gundumar Kukawa da ke tafkin na Chadi a ɓangaren Nijeriya a ranar Laraba a lokacin da masuntan ke ƙoƙarin kama kifi.
Wasu ‘yan bijilanti biyu da ke taimaka wa sojojin Nijeriya yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin sun shaida wa AFP cewa akwai masunta da dama da aka kashe a farmakin.
"Akwai wani hari da wani jirgin sama na sojojin Chadi ya kai wa masunta a tsibirin Tilma wanda ya kashe masunta da dama," in ji Babakura Kolo, wani shugaban mayaƙan sa kai da ke yaki da masu iƙirarin jihadi.
Kolo ya kara da cewa, "Jirgin ya yi kuskuren masuntan da ‘yan ta’addan Boko Haram waɗanda suka kai hari a sansanin soji da ke Chadi a ranar Lahadi,” in ji Kolo.
Da yake neman a sakaya sunansa, wani babban hafsan sojin Chadi ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaran AFP cewa an kai hare-hare a tsibirin da ke kan iyakokin Nijeriya da Nijar.
“Mayaƙan Boko Haram na yawan sajewa da masunta da manoma a lokacin da suke aikata laifuka.
“Hakan ne ya sa lamari ne mai wahala a rinƙa bambance tsakaninsu da ‘yan ta’adda,’ in ji shi.
Baya ga kashe kusan 40, harin da Boko Haram ta kai a ranar Lahadi a sansanin sojin da ke yankin na Tafkin Chadi ya yi sanadin jikkatar gomman mutane inda ‘yan Boko Haram ɗin suka fitar da bidiyo a ranar Litinin suna ɗaukar nauyin kai harin.