Harin dai ya biyo bayan wani hari makamancin haka ne kwanaki biyu da suka gabata wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8. Hoto: AP

Gwamnan Darfur Arcua Minnawi ya zargi kungiyar ‘yan tawaye ta Rapid Support Forces (RSF) a ranar Laraba da kashe fararen hula fiye da 20 tare da raunata wasu a wani hari da ta kai a Al-Fashir, babban birnin jihar Darfur ta Arewa.

A cikin wata sanarwa, Minnawi ya kira harin na ranar Talata da "mummunan kisan kiyashi" da aka yi wa fararen hula.

"Rahotanni na farko sun nuna cewa an kashe mutane 20 baya ga adadin wadanda suka jikkata," in ji shi, yana mai kira da a dauki matakin kare fararen hula.

Hakazalika, wata kungiya mai zaman kanta ta Sudan Doctors Network, ta ce mutane 21 ne suka mutu, yayin da wasu 13 suka jikkata a harin na RSF, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta shiga tsakani domin dakile zubar da jini a Sudan.

An shiga rikici

Sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam na Al Fashir, daya daga cikin mafi girma a yankin na Darfur mai yawan jama'a, shi ma an kai masa hari da makaman roka na RSF a ranar Laraba, a cewar kwamitin da ke kiran kansu da ‘yan gwagwarmaya.

Harin dai ya biyo bayan wani hari makamancin haka ne kwanaki biyu da suka gabata wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8 tare da jikkata wasu 13.

Sansanin, inda UNICEF ta ayyana da cewa yana fama yunwa a watan Agusta, ya kasance cibiyar kula da jinkai. Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar likitoci ta (MSF) sun yi tir da harin da aka kai a baya.

Babu wani sharhi daga RSF a kan batun

Tun a ranar 10 ga watan Mayu, Al-Fashir ke fama da rikici tsakanin sojojin Sudan da mayakan na RSF, duk da gargadin da kasashen duniya suka yi game da muhimmancin jinkai na birnin a matsayin cibiyar gudanar da ayyuka na jihohi biyar na Darfur.

An kashe fiye da 20,000 Sudan ta fada cikin rikici tsakanin sojoji da kungiyar sa kai ta RSF tun daga watan Afrilun 2023.

Fadan dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 20,000 tare da raba sama da mutane miliyan 14 da muhallansu, a cewar alkalumman Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin yankin.

AA