Faustin-Archange Touadera ne ke shugabancin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka tun watan Maris din shekarar 2016.

Ana zaben jin ra'ayin jama'a a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka kan yiwuwar gyara kundin tsarin mulki a ranar Lahadi, wanda idan aka amince, za a daina kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa,

Hakan zai bai wa Shugaba Faustin-Archange Touadera damar sake tsayawa takara a karo na uku a shekarar 2025.

An fara zabar Touadera ne a shekarar 2016 a wa'adin shekara biyar kuma ya sake yin nasara a zabe a shekarar 2020 wanda ya kamata ya zama wa'adinsa na karshe a kan karagar mulki.

Sabon tsarin mulkin zai ba shi damar sake neman sabon wa'adin shekara bakwai, kuma daga nan ne babu wani sauran kayyade wa'adin mulki ga shi ko kuma wani da zai yi takarar kujerar shugaban kasa.

Jam'iyyun 'yan hamayya da wasu kungiyoyin fararen-hula sun yi kira da a kauracewa zaben, inda suka ce da ma an kitsa Shugaba Touadera ya ci gaba da zama a kan kujerar mulki har tsawon rayuwarsa.

An samu karancin fitowar masu kada kuri'a, inda a wata rumfar zabe a arewacin wajen birnin Bangui da safiyar ranar Lahadi aka samu masu kada kuri'a kamar dozin biyu a kan layi, kamar yadda wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.

"Ina fatan abokaina za su fito da yawansu su kada kuri'a. Abin da nake so shi ne kasar nan ta samu kwanciyar hankali da ci gaba," in ji Laurent Ngombe, wani malamin makaranta wanda yake cikin mutanen da suka fara kada kuri'arsu.

Kasar wadda ba ta da teku, wadda kuma girmanta ya kai na kasar Faransa da ke da yawan jama'ar da ya kai miliyan 5.5, tana da albarkatun kasa kamar zinare da lu'u- lu'u da kuma timba.

Ta fada halin rashin tabbas iri-iri, ciki har da juyin mulki a karo da dama da bore, tun bayan da ta samu 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.

Touadera, mai shekara 66, wanda masanin fannin lissafi ne, ya yi kokarin dakile boren da wasu kungiyoyi suke masa a kasar tun bayan kifar da tsohon Shugaba Francois Bozize sanadin wani bore da aka yi masa a shekarar 2013.

Shugaba Touadera ya nemi taimakon Rasha wajen dakile boren da ake masa a shekarar 2018.

Tun daga lokacin ne kusan dakaru 1,500 ciki har da sojojin haya na kungiyar Wagner ta Rasha, aka aika kasar tare da sojojin kasar.

Reuters