"Ana ɓatar da mutane da dama. Ba su san makomar iyalansu ba. An kore su dada gidajensu sau da dama," a cewar Mona Rishmawi./Hoto:Reuters

Ɓangarorin da suke fafatawa a yaƙin basarar Sudan tun daga watan Afrilun 2023 sau da dama suna yin lalata da mata a matsayin wani makamin yaƙi.

Wata mamba a Kwamitin MDD don gano Gaskiya kan Yaƙin Sudan, Mona Rishmawi, ta yi tsokaci kan rahoto game da lalatar da ake yi da mata a Sudan a wata hira da Anadolu.

Rishmawi ta ce yaƙin ya sa mata da yawa sun zama 'yan gudun hijira kuma an tilasta wa da dama yin hijira zuwa wasu ƙasashe su kaɗai saboda an kashe mazansu.

Ana yawan korar matan Sudan daga muhallansu kuma suna fuskantar hatsari da dama a lokacin da suke hijira, in ji ta.

"Ana ɓatar da mutane da dama. Ba su san makomar iyalansu ba. An kore su dada gidajensu sau da dama," a cewarta.

Rishmawi ta ƙara da cewa rikicin ya sa magidanta suna barin yawancin 'ya'yansu da matansu su riƙa kula da kansu su kaɗai.

Matan da mazajensu sakamakon yaƙin suna fuskantar bala'i, inda ake ɗaiɗaita iyalansu, in ji ta.

Mata suna ɓoye lalatar da aka yi da su don gudun tsangwama

Rishmawi ta ce lalatar da ake yi da mata a lokacin yaƙin Sudan ta yi matuƙar yawa har sai da ta kai ga kunnen Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ta ƙara da cewa mata suna fuskantar lalata a yayin da suke tserewa daga gidajensu da kuma lokacin da ake tsare da su a yayin da suka yi gudun hijira.

Da take jaddada cewa ana yin lalata da mata da 'yan mata saboda matsayinsu a cikin al'umma, ta ce, "Matan Sudan waɗanda suka yi ƙoƙarin taimakon sauran mutane da ke buƙatar taimako su ma suna fuskantar yin lalata."

Rishmawi ta ce mata suna ɓoye lalatar da aka yi da su don gudun tsangwama.

"Yana da matuƙar wahala a san adadin matan da aka yi lalata da su, saboda, kamar yadda kuka sani a al'adunmu, ana tsangwamar mutanen da aka yi lalata da su. Akwai iyalai da dama da ba sa so su yi magana a kan mata da 'yan mata da aka yi lalata da su."

Kazalika ana ware matan da aka yi lalata da su daga cikin al'umma, sakamakon yadda ake ɗora alhakin yin lalatar a kansu maimakon mutanen da suka yi lalatar da su, in ji ta.

Rishmawi ta ce matan da suka fuskanci lalata suna fama da matsaloli na rashin lafiya sakamakon gallazawar da ake yi musu.

AA