Ernest Bai Koroma mai shekara 70 ya taba zama shugaban Saliyo daga 2007 zuwa 2018. / Hoto: Reuters

Kasar Saliyo na tuhumar tsohon shugabanta Ernest Bai Koroma da laifin cin amanar kasa da wasu laifuka da suka shafi rawar da ya taka a abin da hukumomin kasar suka kira da yunkurin juyin mulki a ranar 26 ga watan Nuwamba.

Koroma, wanda ya jagoranci kasar da ke Yammacin Afirka tun daga 2007 zuwa 2018, an masa tambayoyi a baya, inda hukumomi a kasar suka ce shi ne ake zargi a hukumance da yunkurin juyin mulkin.

"Ana tuhumar tsohon shugaban kasar da laifuka hudu, wadanda suka hada da cin amanar kasa ," kamar yadda wata sanarwa da Ministan Watsa Labarai Chernor Bah ya fitar.

A ranar Talata, Saliyo ta tuhumi mutum 12 da laifin cin amanar kasa bisa alaka da juyin mulki, daga ciki har da Amadu Koita, wanda tsohon dogarin Koroma ne.

Mummunar arangama

Ana yawan bin Koita a kafafen sada zumunta inda yake yawan caccakar gwamnatin Shugaba Julius Maada Bio.

A ranar 26 ga watan Nuwamba, wasu mahara suka far wa wuraren ajiye makamai da barikin soji biyu da gidan yari biyu da ofisoshin 'yan sanda biyu, inda suka yi arangama da jami'an tsaro.

Mutum 21 aka kashe sannan daruruwan fursunoni suka tsere kafin jami'an tsaro suka shawo kan lamarin.

Wannan rikicin ya jawo fargabar wani sabon juyin mulki a Yammacin Afirka, inda Mali da Burkina Faso da Nijar da Guinea duka suka fuskanci juyin mulkin tun daga 2020.

TRT Afrika