Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS na taron Babban Zauren Shugabannin ‘Yan sanda na Kasashen Yammacin Afirka wato WAPCCO.
Ana gudanar da wannan taro ne a Niamey babban birnin kasar Nijar daga ranar Talata 28 zuwa Alhamis 30 ga watan Maris din 2023.
Wannan taron dai yana bayar da dama ga shugabannin ‘yan sandan yankin su yi musayar shawarwari ta yadda za a ciyar da yankin gaba ta fuskar tsaro.
Wadanda za su halarci taron wannan babban zauren sun hada da jami’an tsaro da ma’aikatan ECOWAS da wakilan hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa wato INTERPOL.
A sakon da kungiyar ECOWAS ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce akwai abubuwa hudu da taron babban zauren zai mayar da hankali a kansu.
Abu na farko da za a yi shi ne bitar shawarwari da aka bayar a zaman da aka yi na baya domin ganin ko an aiwatar da su.
Na biyu kuma shi ne musayar shawarwari da kuma ilimi kan tsaro tsakanin hukumomin tsaro da kuma ma’aikatan ‘yan sanda na Interpol.
Sai kara wa juna sani kan irin gudunmawar da ECOWAS ke bayarwa kan tabbatar da tsaro.
Sannan kuma sai bayani kan ayyukan sakateriyar hukumar da kuma yadda ake samun sauyi a yanayin tsaro.
Yammacin Afirka dai na daga cikin wuraren da ke fama da matsalar tsaro a nahiyar Afirka.
Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijeriya da Nijar na daga cikin kasashen da ke kan gaba wadanda ake kai wa hare-haren ta’addanci, kamar yadda rahoto kan kididdigar tsaro ta duniya ya nuna.