Dubban mutane sun tsallaka zuwa Chadi ta kan iyakar Ader. /Hoto:Reuters

Majalisar Ɗinkin Duniya ta faɗa a ranar Juma'a cewa a shirye take ta fara kai abinci yankin yammacin Darfur na Sudan da yaki ya ɗaiɗaita, bayan gwamnati ta yanke shawarar sake buɗe wata muhimmiyar iyaka da Chadi.

Rufe iyakar Adre na tsawon watanni ta kasance babban abin damuwa ga ƙungiyoyin agaji da ke fafutukar ganin an samu abinci da kayan buƙatu a yankin Darfur, yayin da ake ci gaba da fama da rikici.

Yaƙi ya ɓarke ne a watan Afrilun 2023 tsakanin sojojin Sudan ƙarkashin Shugaban riƙo Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) ƙarkashin tsohon Mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

Rikicin ya haifar da ɗaya daga cikin mafi munin matsalar da mutane suka shiga a duniya.

Miliyoyin mutane suna fuskantar yunwa

Fiye da mutane miliyan 25 - sama da rabin jama’ar Sudan - suna fuskantar matsananciyar yunwa. An ayyana annobar yunwa a sansanin gudun hijira na Darfur.

Shirin Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya WFP ya yi maraba da sake buɗe iyakar Adre, kuma ya ce lokaci na ƙure masa na ceto rayuka.

Mai magana da yawun WFP a Sudan Leni Kinzli ta shaida wa manema labarai a Nairobi cewa, buɗe wannan hanya ta Adre mai matukar muhimmanci zai "ba mu damar kai kayan agaji yankin Darfur mai fama da rikici a Sudan, inda aka tabbatar da yunwa makonni biyu da suka wuce.

“A cikin makonni masu zuwa za a shigar da muhimman kayan abinci ta kan iyakar,” kamar yadda ta bayyyana.

Ta ce "WFP na buƙatar a buɗe duk wasu iyakokin shiga Sudan cikin gaggawa."

An yi lodin ayarin motocin

Ta ce an yi lodin tawaga biyu ta motoci ɗauke da kusan tan 6,000 na abincin mutane kusan 500,000, waɗanda za su nufi yankunan Darfur da ke fuskantar barazanar yunwa, da zarar an samu izinin gwamnati.

Tine, iyaka ɗaya tilo da ta ke tsallakawa daga Chadi zuwa Sudan, kusan wata guda ke nen ba a iya bi ta wajen, saboda ambaliyar ruwa. Motocin WFP 30 sun kasa tsallakawa zuwa yankin Darfur.

Fiye da manyan motoci 50 na WFP masu ɗauke da tan 4,800 na abinci da abinci mai gina jiki suma sun maƙale a wurare daban-daban a Sudan sakamakon ambaliyar ruwa.

Matakin buɗe iyakar ta Adre na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta fara jagorantar tattaunawa a Switzerland da nufin tsagaita wuta da inganta ayyukan jinƙai.

Sojojin Sudan (SAF) ba su shiga tattaunawar ba, wacce ake yi a wani wuri da ba a bayyana ba. Tom Perriello, wakilin Amurka na musamman kan Sudan, shi ne ya shirya taron.

Dubban mutane sun yi gudun hijira

"Buɗe iyakar Adre wani muhimmin sakamako ne a wani muhimmin mataki ne ga ayyukan jin ƙai na kai agaji ga waɗanda suke dai tsananin buƙata da kuma gujewa mummunar yunwa," in ji shi a dandalin sada zumunta na X.

"Muna ci gaba da kokarin da muke yi na tsare rayukan 'yan Sudan a kuma daina harba bindigogi. RSF na nan a shirye don fara tattaunawa; ya kamata sojojin Sudan SAF su yanke shawarar zuwa."

Kinzli ta ce kusan mutane 755,000 suna cikin matsananciyar yunwa, kuma ba su da wani zabi in ban da rayuwa hanyar cin ciyawa da ganye.

"Yana da matukar muhimmanci ga ɓangarorin da ke faɗa da juna su baro fagen daga su dawo kan teburin tattaunawa domin mu samu abinci ya kai ga al'ummomin da ke fama da yunwa a faɗin ƙasar, kafin lokaci ya kure," in ji ta.

TRT Afrika