Wannan ne karon farko da ake gudanar da zaben gwamna a jihohi uku na Nijeriya a lokaci guda/ Hoto: AP

A ranar Asabar din nan ne al'ummomin Kogi da Imo da kuma Bayelsa da ke Nijeriya ke fita rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zabukan gwamnonin jihohin.

Ana gudanar da zabe a jihohin ne domin samun wanda zai maye gurbin gwamnoni masu ci a jihohin wadanda wa'adin mulkinsu yake dab da cika.

A jihar Kogi, mutum 18 ne suke neman kujerar gwamnan amma fafatawa za ta fi zafi ne tsakanin Ahmed Ododo na jam'iyyar APC da Sanata Dino Melaye na jam'iyyar PDP. Ododo yana samun goyon bayan Gwamna Yahaya Bello mai barin gado.

Kazalika a jihar Imo, Gwamna mai ci Hope Uzodimma na jam'iyyar APC ne yake neman yin ta-zarce inda zai fafata da 'yan takara 17. Sai dai za a fi gogayya ne tsakaninsa da tsohon Sakatare na Kasa na PDP, Samuel Anyanwu, da fitaccen dan kasuwa Athan Achonu na Labour Party (LP).

A jihar Bayelsa, za a zuba ido a ga wanda zai yi nasara tsakanin gwamna mai ci Duoye Diri na jam'iyyar PDP da tsohon gwamnan jihar Timipre Sylva na APC.

"Mutum 5,169,692 ne suka karbi katin zabe a jihohin uku sannan wannan shi ne karon farko a tarihinmu da za a gudanar da zabe a rana daya kuma a sassa uku na kasar: Arewa ta Tsakiya (Kogi), Kudu Maso Gabas (Imo) da Kudu Maso Kudu (Bayelsa)," a cewar shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.

Farfesa Yakubu ya kara da cewa hukumarsa ta raba kayan zabe kuma "ba mu da dan takara a zaben da za a gudanar."

A nata banagren, rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce ta baza jami'anta a sassan jihohin domin tabbatar da tsaro a lokacin zabukan, kamar yadda mai magana da yawunta Olumuyiwa Adejobi ya bayyana a sanarwar da ya fitar.

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce za ta sanya kafar wando daya da duk wanda ya tayar da rikici a lokutan zaben Kogi, Imo da Bayelsa./Hoto:Nigeria Police Force.

"Babban Sifeton 'yan sanda yana karfafa gwiwar shugabannin siyasa su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya ta hanyar hana magoya bayansu tayar da tarzoma da kuma tabbatar da bin tsarin zabe ba tare da tunzura wani ba," in ji sanarwar da ya fitar.

Masu kada kuri'a sun bayyana kwarin gwiwarsu wajen gudanar da zabe cikin lumana a jihohin uku.

INEC na bincike kan zargin almundahana a Kogi

Hukumar Zaben Nijeriya INEC ta ce tana gudanar da bincike kan wasu rahotanni da ke nuna cewa an cike takardun sakamakon zabe a wasu mazabu tun kafin soma jefa kuri'a.

Jim kadan bayan soma zabe a Jihar Kogi ne aka fara yada wasu bidiyoyi da hotuna wadanda suke nuna an cike takardun sakamakon zabe na wasu mazabu.

“An ja hankalinmu kan wani rahoto da ke nuna cewa an gano cikakken sakamakon zabe a wasu rumfunan zabe a jihar Kogi. Hukumar ba ta dauki wannan lamarin da wasa ba.

A halin yanzu manyan jami’an mu da aka tura jihar suna gudanar da bincike kan lamarin. Hukumar za ta sanar da hukuncin da ta yanke,” kamar yadda hukumar ta wallafa a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter.

TRT Afrika