Hukumomi sun ce an kashe mutanen ne tsakanin watan Afrilu da Yuni. / Hoto: AFP

Fiye da mutane 6,000 ne aka kashe a Afirka ta Kudu tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni, kamar yadda alkaluman 'yan sanda suka nuna, a daidai lokacin da magance laifuka ke neman zama wata babbar matsala ga sabuwar gwamnatin hadin gwiwa ta ƙasar.

Ministan 'yan sanda Senzo Mchunu a ranar Juma'a ya bayyana cewa an yi wa mutum 6,198 kisan gilla a cikin wata ukun da suka wuce, wanda ya ragu da kashi 0.5 cikin dari a daidai wannan lokacin a shekara daya da ta gabata.

"Wadannan alƙaluma suna ba da labari mai raɗaɗi, wanda ke nuna tsananin ƙalubalen da muke fuskanta," kamar yadda ya shaida wa taron manema labarai a Cape Town.

Fyade, a kasar da ta yi kaurin suna wajen kai hare-hare kan mata da kananan yara, ya karu da kashi 0.6 cikin dari, idan aka kwatanta da irin na watanni uku na bara.

Kasar ta samu jumullar fyade 9,309 tsakanin Afrilu da Yuni.

'Yan sandan sun kuma ce an gano laifukan da suka shafi muggan kwayoyi guda 44,735 sakamakon matakin da 'yan sandan suka dauka a lokacin.

"Mun gudanar da ayyuka masu yawa da suka shafi gungu-gungu na masu miyagun kwayoyi, wanda ya kai ga kama wasu muggan kwayoyi haramtattu," in ji ministan.

A watan da ya gabata, an kama wasu 'yan Mexico uku da 'yan Afirka ta Kudu biyu a lokacin da wasu fitattun 'yan sanda suka kai farmaki kan wani dakin haɗa ƙwayoyi na miliyoyin daloli da aka boye a wata gona mai nisa da ke arewacin Johannesburg.

A wani lamarin na daban, an kama wani dan kasar Rasha tare da wani dan kasar Afirka ta Kudu bayan da ‘yan sanda suka kama buhuna 14 cike da sunƙi na hodar iblis da darajarsu ta kai rand miliyan 252 kwatankwacin kusan dala miliyan 14.

TRT Afrika da abokan hulda