Amadou Ba Senegal ya taba rike mukamin ministan tattalin arziki da na harkokin waje kafin ya zama Firaiminista./Hoto: Reuters

An bayyana Firaiministan Senegal Amadou Ba a matsayin dan takarar hadakar jam'iyyu masu mulki a zaben shugaban kasar da za a gudanar a shekara mai zuwa, bayan shugaban kasar Macky Sall ya goya masa baya.

An sanar da Ba a matsayin dan takara daya tilo na gamayyar jam'iyyun Benno Bokk Yakaar (BBY) a zaben da za a yi a watan Fabrairu na 2024 a yayin taron shugabannin jam'iyyar da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Dakar ranar Asabar.

“Bayan an yi tuntuba mai fadi, wadda ta kasance mai matukar wahala tare da duba yiwuwar gudanar da zaben fitar da gwani wanda 'yan takara da shugabannin gamayyar jam'iyyu suka yi watsi da shi, mun yanke shawarar gabatar da dan takarar da baki ya zo daya a kansa,” a cewar tsohon Firaiminista Moustapha Niasse.

A wata sanarwa da ya fitar Shugaba Sall ya yi kira ga maboya bayansa su goyi bayan Ba wanda ya bayyana a matsayin dan takarar da ke da “kwarewa, mai hada kan jama'a kuma mai sauraren jama'a.”

Ba a yi zaben fitar da gwani ba

A watan Satumbar da ya wuce ne aka nada Amadou Ba, mai shekara 62, a matsayin firaiministan Senegal.

Ya taba rike mukamin Ministan Tattalin Arziki da na Kasashen Waje sannan ya rike mukamin mai tsare-tsare na kasa na gamayyar jam'iyyun da ke mulki a zaben kananan hukumomi da aka yi a farkon 2022.

A watan Yuli ne Sall ya sanar cewa ba zai sake tsayawa takara ba don neman wa'adi na uku na shugabancim kasar, abin da ya kawo karshen rade-radin da aka rika yi cewa zai yi ta-zarce.

Ko da yake mambobin gamayyar jam'iyyun BBY sun yi watsi da gudanar da zaben fitar da gwani, Ministan Harkokin Gona Aly Ngouille Ndiaye ya sanar da yin muabus ranar Asabar jim kadan bayan an bayyana Amadou Ba a matsayin dan takarar jam'iyyu masu mulki, a cewar wasu rahotannin kafafen watsa labaran kasar.

Ana sa rai zai sanar da matakin da zai dauka nan gaba.

AA