Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya sanar cewa ba zai tsaya takara a zaben da za a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun 2024 ba.
Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa 'yan kasar ta talbijin ranar Litinin a fadar shugaban kasa da ke Dakar, babban birnin kasar.
Ya yi jawabin ne yayin da ake ta fargabar cewa zai tsaya takara domin neman wa'adi na uku na shugabancin kasar duk da cewa kundin tsarin mulkin Senegal ya haramta masa yin hakan.
"Ina so na kare mutuncina sannan na yi biyayya ga kalamaina. Wa'adin da na soma a 2019 shi ne na biyu kuma na karshe, wannan shi ne abin da na fada a baya kuma shi ne matakin da na dauka a dare nan," in ji Mr Sall, mai shekara 61.
Shugaba Sall ya bukaci al'ummar kasar su tabbatar da zaman lafiya gabanin zaben da za a yi a shekara mai zuwa.
Ya ce babu wanda ya fi karfin doka, ciki har da 'yan siyasa.
Dan takarar gamayyar jam'iyyu mai mulkin kasar Bokk Yakaar zai samu tagomashi sakamakon wannan sanarwa saboda kotu ta haramta wa dan takrar jam'iyyar hamayya Ousmane Sonko tsayawa takara bayan ta same shi da laifi sannan ta yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekara biyu.
Dattako
Matakin da shugaban kasar ta Senegal ya dauka na kin tayawa takara ya jawo masa yabo daga bangarori daban-daban.
''Matakin nasa wani misali ne ga kasarsa da duniya baki daya,'' a cewar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a sakon da ya wallafa a Twitter.
Ya bayyana "matukar jinjinawa ga Shugaba Macky Sall saboda nuna dattako.''
Su ma shugabannin kasashen Yammacin Afirka sun jinjina wa Shugaba Sall.
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohammed Bazoum ya ce ''Na tabbatar cewa wannan mataki da ka dauka bayan ka yi nazari zai rage zaman dar-dar din da ake yi a fagen siyasar wannan kasa kawarmu.''