Kasar Chadi ta soma kamfe na musamman domin gudanar da kuri’a kan sabon kundin tsarin mulki a kasar, wanda ake ganin hakan zai iya zama zakaran gwajin dafi ga gwamnatin mulkin sojin kasar da kuma zuri’ar Itno da ta shafe shekara 30 tana mulkin kasar.
Shugaban rikon kwarya na mulkin sojan kasar Mahamat Idriss Deby Itno wadda gwamnatinsa ta soma jagorantar Chadi tun daga 2021, ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula da kuma gudanar da zabe a bana kafin daga baya ya daga zaben zuwa 2024.
Sama da mutum miliyan 8.3 da ke kasar da ke yankin Sahel aka kira kan su yi zaben raba gardama wanda aka saka 17 ga watan Disamba a matsayin ranar gudanar da shi, wanda wannan wani muhimmin mataki ne wanda zai kai ga zabe da kuma kafa gwamnatin farar hula.
‘Yan adawa da kungiyoyi masu zaman kansu da masana harkokin siyasa sun bayyana cewa wannan zaben ya yi kama da wata hanya wadda ta za tabbatar da Itno da “zuri’arsa” sun ci gaba da mulki bayan shekara 30 suna mulkar kasar.
“Bayan irin salon da kasar ta dauka, babban batu shi ne barin gwamnatin ta yi gwajin farin jinin da take da shi da karfin iko, wanda za a tabbatar da yawan fitowar jama'a," in ji Issa Job, farfesa a fannin shari'a a jami'ar N'Djamena a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
“Tsarin yadda kasar take ba shi ne abin dubawa ba,” kamar yadda Enock Djondang ya bayyana, tsohon shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta LTDH.
“Duk wadanda suka ki amincewa da wannan mulkin na iya kada kuri’a kan abin da ya gabatar.” Wannan sabon kundin tsarin mulkin ba shi da bambanci da wadanda suka gabata, wadanda suka bai wa shugaban kasa karfin iko.
Kira kan a kaurace wa zaben
Masu goyon bayan gwamnatin mulkin sojin kasar na goyon bayan gwamnatin hadin kai sai kuma bangaren adawa kuna na goyon bayan tsarin fediraliya.
Kungiyoyin adawa masu tsatsauran ra'ayi, wadanda wasu daga cikin shugabanninsu suka yi gudun hijira tun bayan da aka far wa masu zanga-zanga a ranar 20 ga Oktobar, 2022, bayan sun bukaci a kaurace wa abin da suka kira " masquerade."
Abin da aka bayar da shawara shi ne “tsarin zabe daya” domin “ci gaban dangi daya”, kamar yadda kungiyar tuntuba ta ‘yan siyasa suka bayyana mai kunshe da jam’iyyu 20.
A ranar 20 ga watan Afrilu, wasu janarori 15 masu karfi a Chadi suka ayyana Janar Mahamat Deby mai shekara 37 a matsayin shugaban kasar bayan rasuwar mahaifinsa a lokacin da yake yaki da ‘yan tawaye.
Zaben gaskiya da adalci
Mahamat Deby ya yi alkawarin bayar da mulki ga farar hula da kuma barin a yi zaben gaskiya da adalci bayan shafe watanni 18 suna rikon kwarya.
Haka kuma ya yi alkawarin cewa shi da kansa ba zai tsaya takara ba.
Sai dai bayan watanni 18 bayan shawarwari da aka bayar a tattaunawar kasa wadda ‘yan adawa da dama da kuma kungiyoyin ‘yan tawaye suka kauracemawa, sai Mahamat Deby ya tsawaita mulkinsa da shekara biyu.
Haka kuma ya amince wa kansa tsayawa takarar shugaban kasa inda ya musaya kayansa na soji da na farar hula.
Kisan kiyashi
An soma babbar zanga-zanga a Oktobar bara bayan da Mista Deby ya tsawaita mulkinsa, inda jami’an tsaro suka yi amfani da karfi wurin kawar da masu zanga-zangar.
‘Yan sanda sun harbe mutum 100 zuwa 300 har lahira kamar yadda kungiyat ‘yan adawa da kuma kungiyoyi masu zaman kansu suka bayyana, a lokacin da mutane suka gudanar da zanga-zanga N’Djamena da wasu wurare.
Hukumomi sun bayyana cewa kusan mutum 50 suka rasu – daga ciki har da jami’an tsaro shida.