Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ce ta kama mutanen da ake zargin su da kitsa tare da yawan sace mutane a kan Titin Abuja zuwa Kaduna.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Kaduna yayin holen mutanen a hedikwatar rundunar ta Jihar Kaduna, jami’in hulɗa da jama’a Muyiwa Adejobi ya ce cikin wadanda aka kama har da waɗanda ake zargi da kashe ɗaliban Jami’ar Greenfield ta Kadunan.
Ya ce daga cikinsu har da wani “riƙaƙƙen ɗan ta’adda” Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da Mande, da ake zargin shi ne ya kitsa tare da jan ragamar sace ɗaliban Jami’ar Greenfiled da kashe wasun su, da kuma jagorantar yawan satar mutane da ake yi a kan Titin Abuja-Kaduna.
Mista Muyiwa ya ce an kama Mande ne bayan samun wasu sahihan bayanai da aka yi a Rido Junction na ƙaramar hukumar Chikun a kan hanyar Abuja zuwa Kadunan.
Jami'in ya ce mutumin ya amsa cewa shi ne shugaban wani gungu da ke tayar da hankalin mutane a kan Titin Abuja-Kaduna, kuma an sanya shi a jerin riƙaƙƙun ƴan bindiga irin su Dogo Gide da Bello Turji.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an kama bindigogi kirar AK-47 guda 48 a yayin da aka kama Mandi kuma ana ci gaba da kokarin gano masu ɗaukar nauyinsa da kuma masu ba shi makamai.
A ranar 20 ga watan Afrilun 2021 ne aka sace daliban jami'ar Greenfield 20 da malamansu biyu, kwana uku bayan nan kuma aka gano gawar takwas daga ciki, yayin da aka saki sauran mutum 14 din ranar 29 ga watan Mayun 2021, bayan sun shafe wata guda a hannun ‘yan bindigar.
Kazalika kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa jami’an tsaron sun kuma kama wani riƙaƙƙen shugaban ƴan bindigar wanda ya kitsa harin da aka kai Cocin Saint Raphael a Fadan Kamantan a watan Satumban 2023.
Mai taimaka wa ƴan bindiga da harkar lafiya
Rundunar ƴan sandan ta kuma bayyana yadda ta kama wani mutum Shedrack John da ake zarginsa da taimaka wa masu satar mutane da abin da ya shafi kula da lafiyarsu a cikin daji.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya tabbatar da cewa, Sufeto Janar Kayode Egbetokun yana ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da doka da oda, da tabbatar da tsaro da tsaron dukkan ‘yan kasa, da kuma yaki da miyagun ayyuka a fadin kasar.
“Wadannan nasarorin da aka samu a hanyar Abuja zuwa Kaduna a baya-bayan nan na nuna kishin rundunar wajen cika aikinmu na kare rayuka da dukiyoyi. Za a gudanar da irin wannan aikin na musamman a sauran manyan titunan kasar ta hanyar kafa runduna ta musamman da za ta saka ido,” in ji shi.