Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin goma na safe. / Hoto: Sen Bala Mohammed

Aƙalla mutum huɗu suka rasa rayukansu a wurin rububin ƙarbar zakka a Jihar Bauchi da ke Nijeriya.

Rahotanni sun ce turmutsutsun ya faru ne a gaban hedkwatar ofishin Shafa da ke kan hanyar Jos a ranar Lahadi da misalin goma na safe.

Wasu kafofin watsa labarai na Nijeriya sun ruwaito mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Nijeriya reshen Bauchi, Ahmed Wakili yana tabbatar da lamarin inda ya ce an samu asarar rayukan ne sakamakon turmutsutsu wurin rabon zakka.

Sai dai ya ce sakamakon ɗaukin gaggawa da ƴan sandan suka kai wurin, abubuwa sun lafa.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rasuwar wasu ɗalibai a yayin karɓar tallafi a Jihar Nasarawa.

TRT Afrika da abokan hulda