Jami'ai ukun da aka sallama din Insifekta Dahiru Shuaibu da Sajan Abdullahi Badamasi da kuma Isah Danladi / Hoto: Nigerian Police

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta sallami wasu jami'anta uku da ke bai wa fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara daga aiki.

Sanarwar da kakakin rundunar CSP Olummuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Alhamis ta ce an sallami 'yan sandan ne, wadanda ke jihar Kano, kan laifukan da suka hada da amfani da bindiga ba bisa ka'ida ba da wuce gona da iri da rashin da'a da kuma bata harsashin gaske.

A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar ‘yan sandan Nijeriyar ta tabbatar da kama jami'an nata, bayan wani bidiyo ya nuna su suna harba bindiga a sama yayin da suke yi wa mawakin rakiya.

Sanarwar ta ranar Alhamis ta ce jami'ai ukun da aka sallama din Insifekta Dahiru Shuaibu da Sajan Abdullahi Badamasi da kuma Isah Danladi, sun aikata laifin ne a lokacin da suke bakin aiki na rakiyar mawakin a Kano.

"A ranar 7 ga watan Afrilun 2023 a kauyen Kahutu da ke Jihar katsina, sai jami'an suka yi ta harbi sama da bindigogin da ke hannunsu duk da dokar 'yan sanda da ta haramta harbin iska, inda suka yi biris da yiwuwar a iya samun tsautsayi a lokacin saboda taron jama'ar da ke wajen da suka hada har da yara," in ji sanarwar.

Ta kara da cewa: "Wannan lamari ba mugun laifi da rashin kwarewa kawai yake nunawa ba, har da jawo wa rundunar da ma kasa baki daya abin kunya."

A karshe rundunar 'yan sandan ta gargadi dukkan jami'anta da su tabbatar da cewa suna yin aikinsu bisa tsarin da dokoki suka tanada don gudun ketare iyakoki da jawowa kai uku.

Kazalika ta bukaci manyan jami'ai da ke sa ido kan kanana da su tabbatar suna ci gaba da yi wa jami'an da suke lura da su bayani na sanin dokokin aiki da yadda za su kauce wa ketare su.

TRT Afrika da abokan hulda