Ma'aikatar Harkokin Wajen Poland  ta yi "godiya ga dukkan waɗanda suka sanya hannu wajen sakin 'yan ƙasar Poland./Hoto:OTHER

Hukumomin Nijeriya sun saki ɗalibai 'yan ƙasar Poland da jami'an tsaro suka kama a Kano suna ɗaga tutar ƙasar Rasha yayin zanga-zanga kan tsadar rayuwa da aka gudanar a ƙasar a farkon watan nan.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Poland da ke Warsaw ce ta tabbatar da hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba.

"An saki ɗaliban ’yan ƙasar Poland kuma yanzu haka suna Kano," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Poland.

Ta yi "godiya ga dukkan waɗanda suka sanya hannu wajen sakin 'yan ƙasar Poland."

Bayan kama 'yan ƙasar ta Poland, mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen ƙasar ya fitar da sanarwa inda ya yi watsi da zargin da hukumomin tsaron Nijeriya suka yi wa ɗaliban na ɗaga tutar ƙasar Rasha, yana mai cewa sun tsinci kansu ne kawai a wurin da ake zanga-zangar.

Ita ma ƙasar Rasha ta tsame hannunta daga masu zanga-zangar da suka ɗaga tutar inda suka riƙa kira ta kai wa ƙasar agaji.

A ranar 1 ga watan Agusta ne dubban 'yan Nijeriya suka gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa inda suka yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dawo da tallafin man fetur wanda ta cire ranar da shugaban ya kama aiki, lamarin da suke gani shi ya jefa ƙasar cikin ƙarin matsin rayuwa.

TRT Afrika