Shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka sun sake zaɓen Bola Tinubu na Nijeriya a matsayin shugaban ƙungiyar ECOWAS kusan shekara guda bayan ya hau kan muƙamin.
Shugabannin sun ɗauki matakin ne ranar Lahadi a taron da suka gudanar a Abuja, babban birnin Nijeriya duk da yake wasu rahotanni sun ce wasu ƙasashen rainon Faransa sun yi adawa da zaɓen nasa.
Yayin jawabinsa na buɗe taron, Shugaba Tinubu ya bayyana irin ƙalubalen rashin tsaron da ƙasashen yankin suke fuskanta tare da yin kira ga shugabannin ƙasashen ECOWAS su yi "aiki domin ganin an kafa tare da gudanar da dakarun tsaro na ko-ta-kwana a yankin don tabbatar da tsaro da ci gaban tattalin arzikin ƙungiyar."
Ya ce tsarin da ƙasashen yankin suka yi don yaƙi da ta'addanci ya bunƙasa haɗin kai na bayar da horo da musayar bayanan sirri da ɗaukar mataki ya taimaka musu.
"Bugu da ƙari, Ministocin Kuɗi da Tsaro sun gana kwanakin baya a Abuja domin tattara kuɗi don kafa Dakarun Ko-Ta-Kwana na ECOWAS domin bunƙasa ƙoƙarin yaƙi da ta'addanci," in ji Shugaba Tinubu.
Ƙasashen ƙungiyar ECOWAS suna da yawan al'ummar da ya kai miliyan 425, sai dai ficewar da ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka yi daga cikinta ta rage wa ƙungiyar ƙarfi.
Babban ƙalubalen da ke gaban Shugaba Tinubu shi ne haɗa kan ƙasashen da ke cikin ƙungiyar ECOWAS musamman ganin yadda ƙasashen uku suka ce ba za su koma cikinta ba.
A jawabinsa, Tinubu bai ce uffan game da ƙasashen da suka fita daga ECOWAS ba, lamarin da masana diflomasiyya suke gani wani yunƙuri ne na kauce wa sake yin takun-saƙa da su.
ECOWAS ta sanya wa Nijar takunkumai ne bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin farar-hula ta Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata. Hakan ne ya sa ƙasar ta haɗa gwiwa da Burkina Faso da Mali, waɗanda su ma sojoji ne suke mulkinsu.
Ƙasashen uku sun zargi ECOWAS da kasancewa 'yar amshin-shatar Faransa wadda ta yi musu mulkin mallaka, wacce tuni suka yanke hulɗa da ita sanna suka kyautata alaƙa da Rasha.