Azali Assoumani ya shafe shekaru da dama yana shugabanci. / Hoto: Reuters

Shugaban Comoros Azali Assoumani ya samu rauni kadan a wani harin wuka da aka kai masa a ranar Juma'a, kakakin gwamnatin kasar ta ce an tsare maharin.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na rana. (1100 GMT) a Salimani Itsandra, wani gari da ke arewa da Moroni babban birnin ƙasar, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Fatima Ahamada ta shaida wa Reuters cewa, "An dan ji wa Shugaba Azali Assoumani rauni da wuka a yayin jana'izar wani babban shehin kasar.

Ba a dai bayyana dalilin kai harin ba.

Majiyar ta garin Salimani Itsandra ta ƙara da cewa maharin tsohon ɗan sanda ne mai kimanin shekaru 20 da haihuwa.

A watan Mayu, an rantsar da Assoumani a wa'adi na hudu a kan karagar mulki, bayan zazzafan yaƙin neman zaɓe, wanda 'yan adawa suka yi zargin cewa cike yake da maguɗi.

AA
TRT Afrika da abokan hulda