Wani jami’in Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), Filippo Grandi, ya ce ‘yan gudun hijirar Sudan za su iya ketarewa Turai idan ba a ba su isasshen agaji a kasashen da suke samun mafaka.
Tun ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2023 ne dai yaki ya barke tsakanin sojin kasar da kuma rundunar RSF, lamarin da ya raba miliyoyin mutane da gidajensu tare da haddasa asarar dubban rayuka.
Filippo Grandi, Kwamishinan Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), ya ce matsalar da ake ciki a Sudan ka iya sawa ‘yan Sudan su bar kasashe makwabta inda kimanin ‘yan kasar miliyan biyu suka samu mafaka.
"Mun sani sarai cewa wannan yankin na cike da masu aikata laifuka da suke son su yi amfani da damar halin da ‘yan gudun hijiran ke ciki domin karbar kudi a hannunsu su kai su arewacin Afirka zuwa Turai,” kamar yadda Grandi ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Reuters a babban ofishin UNHCR a Geneva.
"Ina neman a kara agaza wa ‘yan gudun hijirar cikin Sudan da wadanda suke kasashe makwabta domin idan ba haka ba za su zama ketara Turai."
Kwararar ‘yan gudun hijira da sauran ‘yan ci-rani, musamman bakin-haure na daga cikin muhimman batutuwa da ke raba kawunan jama’a a wasu kasashen Turai.
Alkaluman da hukumar Kula da ‘yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa karin ‘yan gudun hijiran Sudan suna ketarewa Turai inda mutum 6,000 suka isa Italiya daga Tunisia da Libya tun farkon shekarar 2023.
Wannan ya nuna cewa yawan mutunen ya ninka na shekarar da ta gabata sau shida, duk da cewa har yanzu ‘yan Sudan kadan ne daga cikin sabbin bakin da suke shiga Italiya. "Shin agajin zai hana kowa tafiya? Lallai ba zai hana ba," in ji Grandi, wanda zai halarci taron neman agaji ga Sudan a Paris ranar Litinin.
"Amma tabbas wani dailili ne na da zai rage fasa-kaurin mutane," in ji shi. A wani gefen, ranar Juma’a, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce rikicin Sudan zai yi kamari cikin watanni masu zuwa idan ba a daina yakin ba tare da bai wa masu aikin jinkai damar kai agaji ga mutane.
"Kadan ma muke gani a halin yanzu, kuma yanayin na iya ta’azzara," in ji mai magana da yawun WHO , Christian Lindmeier, yana mai jaddada cewa mutum miliyan 15 na bukatar agajin gaggawa kuma cututtuka irin su kwalara da malaria na yaduwa.
Lindmeier ya ce magungunan da ke kasar kimanin kashi 25 cikin 100 na magungunan da ake bukata ne, kuma kimanin kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na cibiyoyin lafiyar kasar ba sa aiki.