Hukumar da ke kula da sa ido a kan ingancin magunguna a Jamhuriyar Nijar, ANRP ta ja hankalin jama'a da su guji yin amfani da wasu nau'ukan magugunan mura 25 da ake sayarwa a shagunan sayar da maguguna a fadin kasar.
Hukumar ta sanar da hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ta kira a ofishinta a birnin Yamai.
Shugabar hukumar, Dakta Dan Nouhou Barira ta ce sun dauki wannan matakin ne sakamakon wani binciken da suka yi da ya kuma gano cewa wadannan magugunan murar suna da illa sosai ga lafiyar jama'a.
Magungunan sun ma fi yin illa musamman ga yaran da suka haura shekara 15 da mata masu juna biyu da masu fama da ciwon zuciya da cutar hawan jini, kamar yadda hukumar ta fada.
Dakta Barira ta ƙara da cewa mafi yawan masu amfani da wadannan magungunan kan je shago ne kai tsaye don sayen maganin mura ba tare da wata takarda daga likita ba.
Ta ce wannan aikin da hukumar tasu ke yi suna yinsa ne don kare lafiyar al'umma, ta kuma ja hankali musamman a daidai lokacin da ake dab da shiga cikin yanayin sanyi, wanda a wannan lokacin ne aka fi yawan amfani da magugunan mura.
Sai dai hukumar ta ce ta fara daukar matakin janye wasu daga cikin magugunan a shagunan da ake sayar da su, kuma ja hankalin jama'a da su guji shan magunguna barkatai ba tare da izinin likita ba.
Kuma hukumar ta ce a kiyayi sayen magani na kan titi da wadanda ake talla a soshiyal midiya, ta ce yanzu sun fara aiki tare da masu shagunan sayar da magugunan don ganin an dakatar da sayar da su da kuma janye su gaba daya daga shagunan sayar da magunguna a fadin kasar.