An sace ɗaliban a ranar Talata 29 ga watan Janairu a Ekiti. / Hoto: NPF

Rundunar yan sandan Nijeriya ta sanar da ceto wasu ɗalibai biyar da malamansu waɗanda aka sace a Jihar Ekiti.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an ceto ɗaliban da malamansu ba tare da sun samu rauni ba.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 29 ga watan Janairun 2024 a lokacin da motar makaranta ke ƙoƙarin kai ɗaliban Eporo da ke Ekiti.

“Muna jinjina da nuna jin daɗinmu kan ƙoƙarin gwamnati da jami’anmu na ƴan sanda da sauran jami’an tsaro waɗanda suka haɗa da Amotekun da bijilanti da mafarauta da ƴan uwa kan fahimtar da suka nuna da juriya,” kamar yadda ƴan sandan suka bayyana a sanarwar.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake samun hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassan ƙasar.

Rahotanni sun ce satar yaran da aka yi ya faru ne a daidai lokacin da ɓarayi suka kai hari kan wata mota da ke ɗake da wasu sarakunan gargajiya uku a tsakanin Oke-Ako da Ipao Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ajoni.

TRT Afrika