Aƙalla mutum 61 ƴan bindiga suka sace a wani ƙauye da ke Jihar Kaduna a Nijeriya, kwanaki kaɗan bayan sace ɗalibai kusan 300 daga wata makarantar firamare, kamar yadda mazauna garin suka faɗa a ranar Talata.
Shaidu sun ce ƴan bindigar sun kai hari ne ƙauyen Buda da tsakar daren Litinin, inda suka buɗe wuta, wani salo na tsorata mutane.
Ba a samu jin ta bakin kwamishinan tsaro da ƴan sanda ba kan wannan lamari zuwa lokacin wallafa wannan labarin.
Ƙauyen Buda na da nisan kilomita 160 daga Garin Kuriga, inda aka sace ɗaliban firamare a makon da ya wuce.
Wani ɗan garin Lawal Abdullahi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ba ya nan ƴan bindigan suka dira, amma matarsa na cikin waɗanda aka sace.
“Matata na cikin mutum 61 da ƴan bindigar suka sace. Har yanzu muna jiransu su kira mu a kan batun kudin fansa,” Abdullahi ya shaida wa Reuters ta wayar tarho.
"Muna fama da hare-hare tsawon lokaci. Lamarin na ƙara taɓarɓarewa, yana tursasa mazauna da manoma a ƙauyuka suna tserewa zuwa wuraren da babu fargaba," wani mazaunin garin Danjuma ya faɗa.
Hakan na faruwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari kan ɗaruruwan Musulmai a yayin da suke sallar Juma'a a Anguwar Makera da ke yankin Kwasakwasa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka kashe wasu mutane sannan suka yi garkuwa da wasu.
Kwana guda kafin harin na Kaduna, wasu ƴan bindiga sun sace fiye da mutum 200, galibinsu mata da ƙananan yara ƴan gudun hijira a Gamboru Ngala a jihar Borno yayin da suka je daji domin saro itacen girki.
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya bai wa jami'an tsaron ƙasar umarni su "gaggauta" kuɓutar da mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihohin Borno da Kaduna da ke arewacin ƙasar.
An shafe shekaru ƴan bindiga na cin karensu babu babbaka a arewacin Nijeriya, inda suke kai hari kan ƙauyuka da tare ababen hawa a kan manyan tituna da kuma makarantu, duk don satar mutane don neman kuɗin fansa.