Babbar kotun tarayyar Nijeriya

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja babban birnin Nijeriya ta bayar da belin mutum 67 daga cikin 76 da gwamnatin ƙasar ta zarga da cin amanar ƙasa sakamakon zanga-zangar da suka gudanar game da tsadar rayuwa a watan Agusta.

Dubban 'yan ƙasar ne suka gudanar da zanga-zanga a biranen Abuja, da Legas da Kaduna da sauran manyan birane domin nuna rashin jin daɗinsu kan sauye-sauyen da Shugaban Bola Tinubu yake gudanarwa musamman a fannin tattalin arziki bayan ya cire tallafin man fetur da wutar lantarki, lamarin da ya ta'azzara tsadar rayuwar da ake fuskanta.

Sai dai an kama mutane da dama inda aka tuhume su da laifuka daba-daban, ciki har da ɗaga tutar Rasha da neman goyon bayanta da kuma rera waƙoƙin juyin-juya-hali, abin da hukumomi suka ce tamkar cin amanar ƙasa ne.

Yayin da take bayar da belin mutanen, waɗanda suka haɗa da ƙananan yara, Mai Shari'a Obiora Egwuatu ta sanya wa kowannensu sharaɗin biyan naira miliyan 10, da kuma gabatar da mutumin da zai tsaya wa kowannensu, wanda zai kasance ma'aikacin gwamnati mai matakin albashi na 15.

Bayanai daga lauyoyin da suka tsaya wa mutanen da aka gurfanar a gaban kotun sun nuna cewa mutum 27 ƙananan yara ne da shekarunsu ba su kai 18 ba, lamarin da ya janyo zazzafar muhawara a ƙasar.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan Nijeriya Muyiwa Ogunjobi ya ce ana iya gurfanar da kowane mutum a kotun Nijeriya muddin shekarunsa ba su gaza bakwai ba.

Kotun ta tura manya daga cikin mutanen da ake tuhuma zuwa kurkuku, yayin da ta tura yaran zuwa wani gidan kula da kangararrun yara sai ranar 25 ga watan Janairu, inda za a ci gaba da shari'a.

Sai dai lauyoyin yaran sun ce za su koma kotu a makon gobe domin neman sassauci game da sharuɗɗan belin da aka sanya musu.

A nasa ɓangaren, Ministan Shari’a na Nijeriya, Lateef Fagbemi, ya buƙaci rundunar 'yan sandan ƙasar ta gabatar masa da kundin shari’ar mutanen a ranar Asabar domin ya yi nazari a kansa domin ɗaukar mataki.

TRT Afrika