An bai wa babban jami'in Binance Gambaryan izinin barin Nijeriya bayan janye tuhumar da ake masa

An bai wa babban jami'in Binance Gambaryan izinin barin Nijeriya bayan janye tuhumar da ake masa

An soke tuhume-tuhumen da ake yi wa Tigran Gambaryan don ba shi izinin zuwa asibiti a ƙasashen waje.
An soke tuhume-tuhumen da ake yi wa Tigran Gambaryan don ba shi izinin zuwa asibiti a ƙasashen waje. / Hoto: Reuters

Gwamnatin Nijeriya ta janye ƙarar da ta shigar ta shugaban kamfanin Binance Tigran Gambaryan kan zargin halatta kudaden haram, domin ba shi damar zuwa asibiti a kasar waje, kamar yadda lauyan gwamnatin ya bayyana a ranar Laraba.

Gambaryan, wanda Ba’amurke ne, kuma shugaban kamfanin hada-hadar kuɗaɗe na Binance, yana tsare a Nijeriya tun daga karshen watan Fabrairu kuma ana tuhumarsa da karkatar da sama da dala miliyan 35.

Gambaryan da Binance sun musanta zargin.

Amma za a ci gaba da shari''a a kan zarge-zargen ƙin biyan haraji ta daban da ake yi wa kamfanin Binance, mafi girman kamfanin musayar crypto na duniya. Binance ya kuma musanta wadannan tuhume-tuhumen.

Wannan mataki ya biyo bayan bayanan da wani jami’in hukumar gidajen yarin Nijeriya NCoS ya bayar ne, wanda ya bayyana a gaban kotun a ranar ƙarshe da aka saurari ƙarar, wadda Gambaryan bai samu zuwa ba saboda rashin lafiyarsa.

Daga nan ne aka sake ɗage zaman shari’ar zuwa yau talata saboda muhimmancin gaggauta shari’ar.

A yayin da aka koma sauraron ƙarar, lauyar EFCC R. U. Adagba ta shaida wa Mai Shari’a Nwite matakin gwamnatin tarayya na janye ƙarar da ake yi wa jami’in Binance din saboda taɓarbarewar lafiyarsa.

Ta ce bayanan da suka samu kwanan nan daga jam'in hukumar gidajen yarin ta hannun ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro ya nuna cewa jikin Gambaryan ya tsananta sosai ta yadda ko tafiya ba ya iya yi sai a kan keken marasa lafiya.

Adagba ta kuma ce baya ga rashin lafiya, Gambaryan na buƙatar a yi masa tiyata wadda kuma zai ɗauki lokaci yana jinya.

TRT Afrika