'Yan kasar Chadi sun amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar da kimanin kashi 86 cikin 100 a kuri’ar raba gardama da suka kada a makon jiya, kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana a ranar Lahadi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan adawa a kasar ke sukar zaben inda tuni wasu daga ciki suka kaurace wa kuri'ar.
Hukumar zaben kasar ta bayyana cewa kashi 63.75 cikin 100 na masu zabe a kasar ne suka dangwala kuri’a, duk da ‘yan adawa sun ce adadin bai kai haka ba.
“Adadin da hukumomi suka sanar bai kai haka ba,” in ji Max Kemkoye, shugaban wata kungiya ta ‘yan adawa.
‘Magudin zabe’
“A ranar zabe kowa ya ga cewa an kaurace wa kada kuri'ar. “Sun yi magudi a zaben, inda suka rika kara tsawon lokaci da suka sanar a yau,” in ji Yoyana Banyara, shugaban ‘yan adawa na kasar wanda ya rika da’awar “ba a yi zabe ba”.
“Abin kunya ne ga kasar”. Sai dai a nasu bangaren, hukumomin sun ce baya ga wasu “kananan matsalolin da aka samu”, an gudanar da zaben raba-gardamar lafiya.
Sakamakon zaben a halin yanzu na wucin-gadi ne inda ake sa ran Kotun Koli za ta tabbatar ko kin tabbatar da zaben a ranar 28 ga watan Disamba.
Mayar da mulki ga farar-hula
Kuri’ar raba gardamar da aka gudanar wani muhimmin mataki ne na mayar da mulki ga farar hula kafin karshen shekarar 2024, kamar yadda shugabannin sojin kasar suka yi alkwari.
Sai dai shugabannin ‘yan adawa da dama sun bayyana cewa wannan wata hanya ce ta sharar fage ce ga shugaban mulkin sojin kasar Janar Mahamat Idriss Deby Itno domin zama shugaban kasar.