Amurka za ta rage mafi yawan tallafinta ga Nijar 'har sai sojoji sun bai wa farar hula mulki'

Amurka za ta rage mafi yawan tallafinta ga Nijar 'har sai sojoji sun bai wa farar hula mulki'

Tun a watan Agusta ne aka tsayar da tallafin dala miliyan 200 da Amurka ke bai wa Nijar, inda a yanzu kuma aka dakatar da shi gaba daya.
A watan Agusta ne aka tsayar da tallafin dala miliyan 200 da Amurka ke bai wa Nijar, inda a yanzu kuma aka dakatar da shi gaba daya. / Photo: AP

Amurka ta ce za ta rage yawan tallafin da take bai wa gwamnatin Nijar bayan da Shugaba Biden ya ayyana hambarar da mulkin da sojoji suka yi a kasar a matsayin juyin mulki a hukumance.

A watan Agusta ne aka tsayar da tallafin dala miliyan 200 da Amurka ke bai wa Nijar, inda a yanzu kuma aka dakatar da shi gaba daya.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaro ta Amurka Matthew Miller ya ce “Ba za a dawo da bayar da kowane irin taimako ba har sai sojojin juyin mulkin sun mika wa farar hula ba tare da daukar dogon lokaci ba.”

“Mun yanke shawarar cewa za mu ci gaba da ayyukanmu na agaji na ceton rayuka kamar na abinci da lafiya don amfanin al’ummar Nijar. Muna tare da al’ummar Nijar a muradunsu na dimokuradiyya da ci gaba da zaman lafiya,” ya kara da cewa.

Sannan Amurka ta jaddada kiranta ga sojojin Nijar da su saki hambararren Shugaban Kasar Mohamed Bazoum da iyalansa da dukkan wadanda aka kama a lokacin juyin mulkin.

Ko a ranar Litinin din da ta wuce sai da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Blinken ya yi magana da Bazoum ta waya yana jaddada masa cewa “zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya ta fi ba da dama wajen kasancewar Nijar babbar abokiyar hadin gwiwa a tsaro da ci gaba a yankin.

A ranar 26 ga watan Yuli ne Janar Abdourahamane Tchiani, wani tsohon kwamandan rundunar da ke gadin fadar shugaban kasa ya jagoranci hambarar da Bazoum.

An zabi Bazoum a matsayin shugaban Nijar ne a shekarar 2021 a lamari na farko da ya kasance wata farar hula ta mika wa wata farar hular mulki a kasar tun bayan samun ‘yancin kanta a shekarar 1960.

AA