Amurka ta yanke shawarar cewa mambobin dakarun RSF na Sudan da mayaƙan da suke ƙawance da su sun aikata kisan kiyashi a Sudan, kuma ta sanya wa shugaban dakarun takunkumi saboda rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, ya kuma fitar da miliyoyi daga gidajensu.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya faɗa a wata sanarwa cewa mayaƙan RSF da ƙungiyoyin mayaƙa da suke ƙawance da su sun ci gaba da kai wa fararen hula hari kai tsaye.
Mayaƙan sun kuma riƙa kai hari ga fararen hula da suka guje wa yaƙin, sannan sun riƙa yi wa mutanen da ba su ji ba su gani ba kisan gilla, a lokacin da suke guje wa yaƙin, a cewar Blinken.
“Amurka a shirye take ta ɗauki mataki kan duk waɗanda suka aikata miyagun laifuka,” kamar yadda kalaman Blinken suka nuna.
‘Mummuan’ yaƙi
Washington ta sanar da sanya takunkumi kan shugaban RSF, Mohammed Hamdan Dagalo, inda aka haramta masa zuwa Amurka da kuma hana shi taɓa duk wata kadarasa da take Amurka.
“Kusan tsawon shekaru biyu ke nan, mayaƙan RSF na Hemeti suka ɗauki makamai suka tunkari Rundunar Sojojin Sudan don neman iko da ƙasar, inda suka kashe dubban mutane, suka kuma raba ‘yan Sudan miliyan 12 da mahallansu, suka kuma janyo mummunar yunwa,” kamar yadda Baitul Malin Amurka ya faɗa a cikin wata sanarwa daban.
Sojojin Sudan da kuma mayaƙan RSF sun kwashe fiye da watanni 18 suna yaƙi, inda suka jefa mutane cikin ƙangin wahala, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya take ƙoƙarin samar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.
Yaƙin ya ɓarke a watan Afrilun 2023 a lokacin da ake faftukar ƙwatar iko tsakanin Dakarun Sudan da kuma na RSF gabanin miƙa mulki ga farar hula da aka tsara.